Dangote Ya Shiga Cikin Jerin Mutane 100 Mafiya Arziƙi A Duniya

286

Aliko Dangote, mutumin da ya fi kowa arziƙi a Afirka ya shiga cikin jerin mutane 100 da suka fi kowa arziƙi a duniya.

A cewar Bloomberg Billionaires Index, sunan Mista Dangote ya zama na 96 bayan da dukiyarsa ta kai dala biliyan $4.3 a shekarar 2019, sakamakon ribar da yake samu daga hada-hadar siminti, filawa da sikari.

Shahararren ɗan kasuwar ɗan shekara 62 ya je ƙarshen shekarar 2019 da tarin dukiya da ta kusa dala biliyan $15, abinda ya mayar da shi mutum na 96 mafi arziƙi a duniya.

Wannan rahoto ya nuna cewa mafi rinjayen ribar Dangote ya same ta ne daga hannun jarinsa da ya kai kaso 85% da ya zuba a Kamfanin Dangote Cement.

Shi ne yake riƙa da hannun jari a kamafanin kai tsaye ta hanyar gungun kamfanoninsa wato Kamfanonin Dangote.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan