Gaskiyar Magana Kan Ɗaukar Sabbin Ma’aikata a Hukumar NECO

280

Hukumar Jarrabawa ta kasa NECO ta umarci yan kasa da kadasu amince da sanarwar dake yawo tana cewa hukumar na shirin daukar sabbin ma’aikata.

A ciki sanarwar da sahin hudda da jama’a da yada labarai ya Sanyawa hannu, Azeez Sani, yace hukumar bata da shirin daukar sabbin ma’aikata.

“Muna gargadin cewa wannan shiri kawai na masu damfara, wadanda suke shirin damfarar al’ummah” acewar sa.

Inda ya kara da cewa “Hukumar a kar kashin shugabanta na rikon kwarya Abubakar Muhammed Gana, tare da Shugaban hukumar gudanarwar Dr. Abubakar Saddiq Muhammed, masu yin biyayya ne da irin salon shugabancin Muhammadu Buhari na bayyana yin aiki a bayyane, ba tare da boyewa ba.

Daga: Adam Yusuf Hamisu

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan