Hanyoyi 5 Dake Hana Mutum Adana Kudi A Najeriya

428

Abin mamaki sai mutane ke rusa assala suna korafin wai sun kasa samun wadata alahali ko sun bar jaki suna dukan taiki, ai ba samun kadan ne ke dakile arziki ba sam, yadda ka ke ragargazar kudi ne ba gaira ba saban. Wanda da zaka lura sai dalilin su fito ma a fili baro-baro. Wadanan kananun abubbuwa 5 da ka raina sune jagororin hana ka tara kudi.

1- Wayar hannu ko tafi da gidan ka
Ba jayayya akan amfanin wanan wayar hannu ga rayiwar mutane, wace ta zamo takalmin kaza mutu karaba, ko wane lokaci muna maƙe da ita. Sai dai kash, mafi yawan ƴan Najeriya suna salwantar da maƙudan kuɗi wajen malakar wayar selula ɗin daga sabuwar salon waya ta fito sai su garzaya su tatuƙe asusu su saya, mai iPhone 8 ya koma X mai XI ya koma 12 duk da cewa amfani ɗaya tak suke yi.

2 -katin waya domin ƙira ko sayan data
Abin bai tsaya ga sauya wayoyi ba kaɗai yawan sa katin ƙira na ɗaya daga cikin hanyoyi da koban mu ke sulalewa su bar mu tik, wadda ga dukkan alamu masu kamfanonin sadarwa na matuƙar amfanuwa daga yadda muke jibga kuɗin mu wajen sanyan kati da datar hauwa yanar gizo, abin takaici sai mutum ɗaya kashe tamkar dubu biyar (5,000) a wata guda domin sayan data. Muna sha’awar taƙaita kisan kudi amma hotonan Instagram, bidiyon yoututube gami da status ɗin WhatsApp basu bar mu ba.

3 zuba mai a janerato da motar hawa
A kasar nan ne fa zaka kashe naira dubu 10,000 domin more subkirifshin ɗin dubu 2,000 na GoTv bayan haka kuma tilas ka biya kuɗin wuta wani, ƙarin raɗaɗi da zurarewar sulalla daga aljihu, abu mafi sauki anan shine hauwa motar haya duba da masifar tsadar fetur wadda lita ɗaya rak ta kai 145.
4- kwankaɗar barasa
Duba ga tarihi a Najeriya ana samun yawan kwankwadar barasa, Inda matasa ke lafta makudan kudin da suka sha wuya wajen nema donin durkar barasa a banza a wufi.
5- biyan kudin sufuri
Ba wanda zai addar ma da wanan yankan kauna na lankwame kudin safara face mazauna garin Ikko, duban ‘yan Nijeriya ka dunguma can wata uwa duniya nesa da matsugunar su zuwa da dawu kullum. Ga tsadar tsiya musaman idan mahaiya na da yawa dai dai lokacin dawowa gida daga wajen aiki.Mafi tsoka daga kudin da ke samun na shekewa ne ta hanyar tafiya da dawowa daga aiki.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan