Badia Ibraheem Zakzaky, ‘yar Ibrahim El-zakzaky, Shugaban Ƙungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta Najeriya, IMN, wadda aka fi sani da Shi’a, ta bayyana damuwarta bisa yanayin lafiyar mahaifinta bayan an mayar da shi Babban Gidan Gyaran Hali na Kaduna.
“Makonni uku da suka gabata, sun (hukumomin Najeriya) mayar da Sheikh Zakzaky zuwa Babban Gidan Gyaran Hali, alhali ba shi da cikakkiyar lafiya, kuma ba a ba shi dama ya sha magungunansa ba, ya kuma ziyarci likitocinsa ba.
“Suna son su kashe Sheikh Zakzaky, kuma sun takura da fusata gidanmu sosai”, Misis Badia ta faɗa wa Kamfanin Dillancin Labarai na AhlulBayt haka ranar Laraba.
Wani lokaci a 2015, jami’an Rundunar Sojin Najeriya suka yi dirar mikiya a Zariya, inda suka cafke Mista El-zakzaky, wanda ya kusa shekara 70.
An yi artabu a gidan Mista El-zakzaky dake Zariya, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mabiyansa fiye da 300, da kuma ‘ya’yansa uku.
Haka kuma, Mista El-zakzaky ya rasa ɗaya daga cikin idanunsa, matarsa kuma ta samu mayan raunuka.
Tun lokacin ake tsari da shi da matarsa da tarin mabiyansa.
A ranar 5 ga Disamba, 2019, wata Babbar Kotu ta umarci Sashin Rundunar Tsaro ta Farin Kaya, SSS, da ta mayar da Mista El-zakzaky da matarsa, Zinat zuwa Gidan Gyaran Hali na Jihar Kaduna.
Su ma ‘yan Shi’a sun bayyana damuwa bisa sauya wa El-zakzaky waje, suna masu cewa duk wani yunƙuri na sauya wa Mista El-zakzaky da matarsa wani waje ba asibiti ba zai ƙara jefa su ne cikin haɗari.
IMN ta ce kayan aikin da suke Babban Gidan Gyaran Hali na Kaduna tsofaffi ne, suna masu ƙarawa da cewa Gidan Gyaran Halin shi ne gidan da waɗanda suka tsira a artabun watan Disamba da aka kai su suka mutu bisa rashin kulawar likitoci.
A bara, IMN ta zargi Gwamnatin Najeriya da zuba wa Mista El-zakzaky guba, bayan an samu “sinadaran lead da cadmium masu tarin yawa a jininsa”.
A watan Agustan bara, a wata tattaunawa ta musamman da FNA, Dakta Pourrahim Najafabadi, MD, ya ce Mista El-zakzaky yana buƙatar samun kulawa daga tawagar ƙwararrun likitoci a wani ƙwararren asibiti mai ɗimbin likitoci a wajen Najeriya, tunda duk nahiyar Afirka babu irin wannan asibitin.