Idan Kun Samu Labarin Mutuwata Atiku Ne – Walid Jibirin

410

Shugaban kwamitin dattawa na jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin ya jawo hankulan jama’a ta yadda magoya bayan tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar ke barazana ga rayuwarshi a kan tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023.

Ya sanar da hakan ne a zantawar da yayi da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 2 ga watan Janairu.

“Ina samun kiran waya daga wasu mutane masu barazana ga rayuwata a kan yankin da ya kamata a ba takarar shugaban kasa. Sun ce na ci amanar yankin Arewa maso gabas kuma da Atiku kadai nake.”

“A halin yanzu ba mu tattauna a kan yankin da za a ba takara ba, a kan me suka damu da inda za a ba tikitin? Wasu mutane uku sun zo jerin kantuna na Wadata kuma sun bukaci gani na. An kirani a waya na shaida musu ina Kaduna. Sai suka sanar cewa wasu ‘yan siyasa ne suka turo su. Matukar ban shiga taitayina ba, zasu hada ‘yan ta’addan da zasu yi min aika-aika.

“A take nace musu suje suyi abinda duk zasu yi, na shirya. Daga nan ne na gano cewa suna nufin kasheni ne.”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan