Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana asalin tarihin rayuwarsa, inda ya bayyana cewa iyayen da su ka haifeshi cikakkun jahilai ne, kuma an haifeshi ne a wani ƙaramin ƙauye mai suna Ibogun – Olagun.
Obasanjo ya ƙara da cewa amma hakan bai hana sh yin kokarin magance duk wata matsalar da za ta hanashi zama shugaban ƙasar nan a zamanin mulkin soja da kuma zamansa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa farar hula tsahon shekaru takwas.
Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a lokacin da ake taron shekara na gudanar da addu’ar ƙungiyar kiristoci ta ƙasa CAN reshen jihar Ogun.
“Wasu daga cikinku sun san inda aka haifeni, amma mutum nawa ne su ka san Ibogun – Olaogun? To shi ne ƙauyen da aka haifeni, kuma ƙaramin ƙauye ne domin duk yadda za’a fadada taswirar ƙasar nan to ba zai taba fitowa a cikinta ba”
“Amma duk da haka Ni da cikakkun jahilan iyayena su ka haifa a wannan ƙauyen na samu damar da na ke da ita yanzu, kuma na kai matsayin da na cimma duk wani buri nawa, to ya kuwa ba zan godewa Allah ba? ” in ji Obasanjo

Hakazalika Obasanjo ya ce a kullum yana godewa Allah akan irin damar da ya bashi ya cimma burinsa, haka kuma yana kara godewa mutanen da su ka taimake shi ya cimma burinsa na rayuwa. Duk da cewa wadansu sun mutu, amma wadansu suna nan da ransu.
A ƙarshen taron adduar gwamnan jihar Ogu Mista Dapo Abiodun ya bayyana tsohon shugaban ƙasar a matsayin shugaba mai tsoron Allah da ya kamata a yi koyi da shi