Ɗan Kwankwasiyya Ne Ya Haɗa Bidiyon Bogi Na Auren Buhari da Sadiya- DSS

427

A ranar Juma’a ne Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, SSS ta kama mutumin da ake zargi da ƙirƙirar tare da yaɗa bidiyon bogi na ƙarya, wanda ya nuna Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya auri Ministarsa ta Ayyukan Jin Ƙai, Sadiya Umar-Farouq.

Da yake holin wanda ake zargin a Hedkwatar Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Ƙasa ranar Juma’a, Jami’in Huɗɗa da Jama’a na Hukumar, Dakta Peter Afunanya, ya ce wanda ake zargin, wanda ya amsa laifin ƙirƙirar da kuma yaɗa faya-fayan bidiyon na bogi, ɗan wata ƙungiyar siyasa ne da ake kira Kwankwasiyya a Kano.

A cewar Mista Afunanya, an ƙaddamar da bincike ne bayan da Ministar Ayyukan Jin Ƙai ta shigar da ƙorafi ga hukumar a hukumance.

Ya ce: “Bara, 2019, tsakanin Agusta da Oktoba, akwai bidiyo na ɓata suna da da ya karaɗe faɗin Najeriya, wanda ke nuna ƙaryar cewa Shugaban Ƙasa ya auri wasu daga cikin ministocinsa.

“Ɗaya daga ciki shi ne na Ministar Kuɗi, Hajiya Zainab Ahmed, ɗayan kuma shi ne na Ministar Ayyukan Jin Ƙai Da Walwalar Jama’a, Hajiya Sadiya Farouq.

“Ranar 11 ga Oktoba, 2019, Ministar Kuɗi ta shigar da ƙorafi ga Hukumar a hukumance, inda ta bayyana cewa bidiyon ya kunyata ta sosai, kuma ta roƙi a gudanar da binciken wannan saƙon murya/ da na bidiyo da kayayyakin dake tare da bidiyon da hotunan dake da shi da gaba ɗayan kayayyakin dake tare da shi dake ci gaba zagayawa a lokacin.

“Ta roƙi cewa a gudanar da cikakken bincike a kan wannan al’amari don gano mutanen ko gungun mutanen da suke da alhakin yaɗa waɗannan faya-fayan bidiyo masu ɓata suna.

“Hukumar ta fara bincike, kuma a yanzu za mu iya sanar da cewa ta kama mutumin da yake da hannu da ma mutumin da ya fara da wanda ya haɗa bidiyon.

“Sunansa Kabiru Mohammed. Ɗan Kano ne. Shekararsa 32. Yana da ‘Diploma’ a Hausa da Fulfulde daga Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya dake Kano, FCE Kano, da kuma ‘Diploma’ a Ilimin Aikin Jarida daga Kwalejin Nazarin Addinin Musulunci da Shari’a ta Aminu Kano.

“Ya amsa laifinsa kuma bincike ya tabbatar yana da hannu a ƙirƙirar waɗannan faya-fayan da kuma yaɗa su.

“Ana ci gaba da bincike don gano ainihin dalilai da suka sa ya yi haka. Abinda za mu iya tabbatar wa ‘yan Najeriya shi ne za mu ci gaba da zurfafa wannan bincike har mu ga ƙarshensa.

“Za mu yi dukkan abinda ake buƙata cikin tanadin doka don ganin mun kammala wannan bincike zuwa ƙarshe, kuma mu gano ko akwai wani mutum ko mutane ko kuma babu, ƙungiyoyi da manufofi fiye da suka sa aka yi haka, fiye da abubuwan da ya faɗa.

“Muna son yin amfani da wannan dama mu ƙara yin kira ga ‘yan Najeriya kamar yadda muke yi koyaushe cewa yaɗa labaran ƙarya ta kafafen sada zumunta na zamani ba ya amfanar kowa. Za ka iya jin daɗin yaɗuwar irin waɗannan ƙarairayi idan ba kai abin ya shafa ba. Amma idan kai abin ya shafa, za ka ji raɗaɗin da ake ji.

“Kuma muna so mu yi kira ga ga duk ɗan ƙasa da mazauna Najeriya da ma ‘yan Najeriya gaba ɗaya, cewa a duk inda suke, su guji yaɗa ƙarya, bayanai masu rikitarwa, jita-jita a kan juna, a kan gwamnati da ma cibiyoyin gwamnati.

“Daga lokacin da ka danna wannan maɓalli, ka yaɗa ko ka bada gudunmawa wajen yaɗa labari da ba na gaskiya ba, kana taimakawa ne wajen haifar da tashin tashin-tashina, kana taimakawa wajen kawo matsala a ƙasa. Kuma kana amfani da bambance-bambancen da ake da su a ƙasa don kawo hargitsi, karyewar doka da oda da rashin zaman lafiya.

“Kamar yadda muka shiga Sabuwar Shekara, muna kira ga kowa da ya koyi wata sabuwar ɗabi’a, ya kuma nemo dalilai da za su sa ya zama ɗan kishin ƙasa sosai, ya zama mai kiyaye doka sosai kuwa mutane su zama ‘yan ƙasa na gari, sannan su taimaka a ciyar da Najeriya gaba.

“A ɓangarenmu, za mu ci gaba da yin ayyukanmu da sauke nauyaye-nauyaye da suke kanmu yadda ya dace, ba tare da son kai ko tsoro ba, kuma koyaushe za mu ci gaba da haɗa kai da dukkan masu ruwa da tsaki musamman kafafen watsa labarai da sauran muhimman abokan aiki don tabbatar da samun zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar nan”, in ji Mista Afunanya.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan