Masu Zuwa Ƙasashen Ƙetare Neman Lafiya Na Ɓata Min Rai- Buhari

552

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nuna ɓacin ransa bisa halin da asibitocin Najeriya ke ciki, yana mai cewa ƙasar nan ba za ta ci gaba da sa ido tana ganin ‘yan Najeriya na fita waje ba don neman lafiya.

A cewar jaridar PUNCH, Shugaban Ƙasar ya bayyana haka a yayin ƙaddamar da ayyuka a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Alex Ekwueme dake Abakaliki, jihar Ebonyi ranar Juma’a.

Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin Ogbonnaya Onu, Ministan Kimiyya da Fasaha, ya ce yawan tafiya ƙasashen ƙetare don neman lafiya ba ya amfanar ƙasar nan, yana mai ƙarawa da cewa dole a kawo ƙarshen haka.

“‘Yan Najeriya sun sha wahala sosai saboda tafiya ƙasashen ƙetare neman magani. Wannan ba abu ne mai kyau a gare mu ba, kuma dole a daina haka saboda ba za mu iya ɗaukar nauyin haka ba”, in ji shi.

Ya ce wannan aiki a asibitin ya zama wajibi don a kawo wa mazauna jihar sauƙi, kuma a inganta lafiyar mazauna Kudu Maso Gabashin Najeriya.

Shugaban Ƙasar ya ce gwamnatisa a jajirce take wajen kawo ci gaba a kowane ɓangare na ƙasar nan.

“Mun bada kulawar gaske ga lafiyar al’ummarmu kuma za mu ci gaba da yin haka. Ayyukan da kuke murnar kammalarsu yau sun yi tasiri sosai ga aikace-aikacen wannan asibiti”, in ji Shugaba Buhari.

“Amma yau, za mu iya cewa kammalarsu ta fara taimakawa wajen bunƙasa ƙwazo da jin daɗin ma’aikata da marasa lafiya na wannan asibiti.

“Ina son yin amfani da wannan kafa in taya Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha murna da wakilansa a ‘Ofsihin Ecological Fund’, ɗan kwangilar da ya yi aikin, Messrs Amayaro Nigeria Limited da kuma ƙwararre a kan aikin, Messrs Kanode and Associates Limited, bisa jajircewarsu don tabbatar da cewa an kammala aikin a kan lokaci”, ya ƙara da haka.

Shugaban Ƙasar, wanda ya sha suka bisa neman lafiya a ƙasashen ƙetare, ya shafe fiye da kwanaki 150 yana karɓar magani a wata rashin lafiya da ba a bayyana ba a Landan a 2017.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan