Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Ƙarin Kuɗin Wutar Lantarki

249

Hukumar Kula da Rarraba Wutar Lantarki ta Najeriya, NERC, ta amince da ƙarin kuɗin wutar lantarki da Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki, DisCos 11 na ƙasar nan suka yi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ya bada rahoton cewa an wallafa wannan umarni na sabon ƙarin kuɗin wutar lantarkin ga DisCos da ajin masu amfani da wutar lantarki daban-daban a shafin Intanet na NERC ranar Asabar.

Shugaban NERC, James Momoh da Sakatarenta, Dafe Akpedeye su suka sa wa umarnin hannu.

Hukumar ta ce wannan umarni na baya ya shafe na baya ta ta bayar game da ƙarin kuɗin wutar, kuma “kuma sabon ƙarin kuɗin wutar ya fara aiki ne tun 1 ga Janairu, 2020”.

A cewar jaridar Intanet ta Legit.ng Hausa, Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki, DisCos da ƙarin ya shafa su ne: Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja, AEDC, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Benin, BEDC, Rarraba Wutar Lantarki na Enugu EEDC, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Eko, EKDC, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ibadan IEDC, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ikeja, IEDC, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Jos, JEDC, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna, KEDC, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano, KEDCO, Kanfanin Rarraba Wutar Lantarki na Fatakwal, PEDC da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Yola, YEDC.

Legit.ng Hausa ta ƙara da cewa ƙarin zai kasance kamar haka:
Ikeja: Daga N13.34 zuwa N21.80 ga kowane Kilowat, KW ɗaya
Enugu: Daga N17.42 zuwa N30.93 ga duk KW ɗaya
Abuja: Daga N27.20 zuwa N47 ga duk KWh ɗaya

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan