Matasan su biyu abokan juna masu kimanin shekaru 25 a duniya sun rasa ransu bayan sun kunna wutar garwashi a dakinsu, sakamakaon wani muku mukun sanyi da ake yi a birnin jos.
Matasan mazauna yankin unguwar Gangare a ƙaramar hukumar Jos ta arewa sun rasa ransu ne a ranar juma’a da daddare bayan sun dawo gida da misalin ƙarfe 12 na dare, sakamakon shaƙar hayakin wutar da su ka kunna da nufin dumama dakin da su ke kwana
Tun da farko wani mai suna Alhaji Labiru ɗan uwa ga ɗaya mamacin ya bayyanawa manema labarai cewa, ƙanin nasa tare da abokinsa sun rasu ne a gidansa bayan sun kwanta a ɗakinsu da ke ƙofar gida a ranar juma’a, bayan da su ka kunna wuta a dakin da su ke kwana.
Tsananin sanyi dai a garin Jos din da ke jihar Filato ya takura jama’a, yadda da dama suka kasance a cikin daki suka kasa fita gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Tun ranar Laraba, daya ga watan Janairun 2020 ne matsanancin sanyi ya sauko a sassa daban-daban na Arewacin ƙasar nan.
