Home / Labarai / Babu Haɗi Tsakanin Sanyin Kano Da Na Ingila – Aliyu Salisu Barau

Babu Haɗi Tsakanin Sanyin Kano Da Na Ingila – Aliyu Salisu Barau

Wani masanin muhalli daga Jamiar Bayero da ke Kano Dakta Aliyu Salisu Barau ya bayyana cewa sanyin da ake yi a Kano ba shi da kamanceciniya da sanyin da ake yi a ƙasar Ingila.

Aliyu Salisu Barau ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da filin Barka da Hansti da ake gabatarwa a tashar Freedom Radio, da ke Kano.

Daktan ya ƙara da cewa wasu daga cikin al’umma suna yin kuskure wajen fassara yadda yanayin sanyi ke kasancewa. Yace ma’aunin Celsius a mataki na 9 da ake cewa Kano ta kai matsayi ne na ma’aunin sanyi da Kano kadai zata iya kaiwa.

Ya kuma ce hasashen da wasu su ke bayyana wai za’a samu zubar dusar kankara a Kano ba gaskiya bane.

Amma irin sanyin da ke faruwa a wannan sati a Kano lokacin sanyi ne da ke tahowa daga arewa kuma iska ce busashshiya saboda haka tana dauke da sanyi mai tsanani ba kamar iska mai tahowa daga Kudu ba.

Bayan haka yace a sati biyu da suka wuce akwai bayanai da suke bayyana cewa za’a samu irin wannan sanyi a nan Kano da wasu sassan arewacin Najeriya.

Idan za’a iya tunawa dai a ƴan kwanakin nan wasu bayanai ke zagawa a kafofin sadarwa na zamani cewa sanyin da ake yi a Kano ya fi na Ingil.

A ƙarshe Dakta Aliyu Salisu Barau ya yi kira ga al’umma da su kiyaye a lokutan da su ke muamala da kayan wuta da sauran abubuwan da za su iya haifar da gobara.

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *