Hisbah Ta Musanta Kama ‘Yan Luwaɗi A Kano

216

Rundunar Hisbah ta Jihar Kano ta musanta rahotonnin kafafen watsa labarai dake cewa ta kama ‘yan luwaɗi 15 ranar Alhamis a yayin wani taro.

A wata tattaunawa ta musamman da jaridar KANO FOCUS, Mataimakin Kwamanda Janar na Rundunar, Mai Kula da Ayyuka na Musamman, Shehu Tasi’u Ishaq ya ce rundunar ta kama wasu maza ne masu shigar mata, ba ‘yan luwaɗi ba.

Wasu kafafen watsa labarai sun bada rahotonnin dake cewa Hisbah ta kama wasu ‘yan luwaɗi, waɗanda aka ce suna bikin kammala jami’a.

Amma Mista Ishaq ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a wani bikin tunawa da zagayowar ranar haihuwa.

“Mun karanta labarin da yake yawo a jaridu da kafafen sada zumunta na zamani cewa Hisbah ta kama ‘yan luwaɗi a Kano, amma yadda labarin yake shi ne ranar 1 ga Janairu, rundunar ta karɓi samu sanarwa dake cewa wasu matasa na shirya bikin tunawa da zagayawar ranar haihuwa a Gandun Albasa, a cikin birnin Kano.

“Mun je wajen, muka kama su, sannan muka kawo su ofishinmu a Sharaɗa”, in ji shi.

Mista Ishaq ya ce rundunar ta miƙa waɗanda ake zargin zuwa ga iyayensu bayan ta ba su shawarwari.

A cewarsa, mutanen da Rundunar Hisbah ke gabatarwa gaban kotu su ne waɗanda suka yi laifi fiye da sau ɗaya.

Daga nan sai ya yi kira ga iyaye da su ba ‘ya’yansu tarbiyya irin ta addinin Musulunci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan