A yanzu lokaci ne da ake tsananin hunturu a wasu sassan Kudu maso Gabashin nahiyar Asiya, don haka aka samar da bargon da ake sakawa da hannu don a taimaki jariran giwaye su ji dumi.

A wannan makon ne aka fara tsananin hunturu a China da ma wasu kasashe irin su Thailand da Myanmar da kuma Cambodiya, irin sanyin da ba kasafai yake tsanani haka irin haka ba,” in ji Lek Chailert, shugaban wata Gidauniyar taimakon giwaye ta Save Elephant Foundation. Gidauniyar na samar da mafaka da dama, da suka hada da wannan da ke Baan Lao, a Myanmar, inda da daddare tsananin sanyin wajen ke kai wa 0C a matakin salshiyas – irin sanyin da ke addabar giwayen da suka tasa balle jariransu.

Wani mai magana da yawun gandun daji ya shaida wa BBC cewa ana kunna wuta da daddare a tsaunkan da ke kewaye da mafakar. Ya ce: “Muna bakin kokarinmu don sa dabbobin nan su ji dumi.” Gidauniyar Save Elephant na ceto dabbobi daga galabaita su samar musu wajen fakewa.

Wasu masu aikin sa kai na kungiyar ne ke saka wadannan kayatattun barguna don taimakon jariran giwaye da gwanki. Suna saka bargunan ga dabbobin da suka rasa iyayensu.
Ya ya ku ka ga bargunan da wadannan giwaye ke lullube da su? Wadannan giwayen suna tare da juna a yayin da suke zagayawa a gandun dajin da ke Myanmar.
Kuma ba jariran giwaye kawai ake sanya wa bargunan ba. A kusa da birnin Chiang Mai, da ke Thailand ma a kan lullube manyan giwaye da barguna, saboda ana tsananin sanyin da ke kai wa maki 8C a matsakin salshiyas. Mai magana da yawun kungiyar ya ce: “A gandun dajin Elephant Nature Park ma mu kan lullube manyan giwaye da barguna saboda kare su daga tsananin sanyin da ke sauka da safe.”
An yada hotunan sosai kuma an kalle su a shafukan sada zumunta na ENP. Wata mata ta rubuta a shafin Facebook cewa: “Kai wadannan giwaye sun yi kyau sosai cikin bargunan nan.” Wata kuma ta rubuta cewa: “Da ganin giwayen suna cikin farin ciki sosai.”
Daga Shafin BBC Hausa
[…] Muƙalar Da Ta GabataYadda Ake Lullube Giwaye Da Bargo Saboda Tsananin Sanyi […]