Muhimmanci Lokaci A Rayuwarmu Ta Yau Da Kullum

62

Lokaci dai na daga cikin abubuwa mafi muhimmanci a rayuwar bil’Adama la’akari da yadda idan ya wuce to ya shude kenan har abada. Wannan yasa mutane masu azanci ke yin amfani dashi a cikin Karin magana irin su “lokaci akan sallata,” “komi da lokacin sa,” “yau da gobe taki wasa,” “akwana a tashi,” “komi nisan dare…” da dai sauran su, domin ankarar da ma’abota hankali matsayin da lokaci ke dashi ga rayuwar bil’adama.

Managartan mutane kanyi kyakkyawan amfani da lokutan su wajen gudanar da rayuwar su cikin sauki da tsari, wanda hakan kan taimaka kwarai wajen kai su ga comma burikan su na rayuwa.

Abu ne sannan ne cewar kowanne dan’Adam dake bayan kasa zai rayu ne na wasu takaitaccen adadi na lokaci wanda ka iya zama shekaru, watanni, kwanaki, sa’o’i, mintuna ko kuma dakikoki kididdigaggu. Kenan a wadannan kididdigaggun lokuta na rayuwa dan’Adam na matsawa kusa da mutuwar sa ne, sai dai kuma shagulgula da hidindimu na rayuwa man sanya mutane su manta da cewar suna rayuwa ne dkmin riskar wa’aid wanda ke raguwa cikin sauri a duk shudewar dakika.

A cikin wadannan kididdigaggun lokuta ne ma’abota neman ilmi, kudi, sarauta ko mulki kan bazama nema, wasu suyi nasara wasu kuma suci karo da akasin haka to amma mutane masu tsari wajen tafi da lokutan su ne su kafi samun saukin gudanar da rayuwa tare da cimma burinka su a wannan duniya mai abin mamaki.

Daga daya gefen kuma akwai sakarkaru da gafallallun mutane wadanda Ba kasafai sukan ankara da muhimmanci lokaci da kuma asara da danAdamkan tafka idan yayi wasa da wa’adin sa ba. Irvin wadannan mutanr na bata wa’adin su na zaman duniya a sabgogi da ba zasu amfani duniyar su ballantana kuma lahira.

Abu daya kamata a kullum mu lura shine rayuwar duniya na gudana ne bisa tsarin wa’adi wanda aka gina tun farko akan gwadabe na shudewa. Babu tsumi babu dabara game da wucewar wannan kayyadajen wa’adi mai matukar gajartar zango, sannan kuma babu batun jinkiri da zarar wannan wa’adi ya cika. Kenan akwai shekaru masu zuwa a nan gaba da zai zamto babu wani mahaluki dake rayuwa a yanzu a doron kasa da zai riske shi, koda kuwa yau aka haifi mutum.

Shekaru dari biyu baya akwai mutane a garuruwan mu kai har ma zuri’ar da muka fito daga ciki, akwai manyan malumma, hamshakan attajirai da ‘yankasuwa, mashahuran sarakuna, kasurguman barayi, ftattun mawaka, manya manyan tantirai, fitattun karuwai da gogaggun ‘yan daudu da ‘yan caca, fitattun mashaya, manyan munafukai da fasikai, zaratan samari da kyawawan mata, amma a yau duk sun shude babu su tamkar ba’a ma taba yin su ba. Kuma dayawa daga cikin wadannan mutane ko a tatsuniyar Gizo da Koki ba zakaji an ambace su ba saboda watakila sunyi wasa da lokaci.

Daga cikin su tarihi kanyi adalchi ne kadai ga wadanda suka wa kansu adalchi ta hanyar yin kyakkyawan amfani da lokacin su, yayin da wadanda idanuwan su suka rufe suka sheke ayar su son ran su kan zamto wadanda tarihi kan fadi aibun su kamar dai yadda ya wakana lokutan rayuwar su.

Shawarar dai itace yakamata mu nutsu muyi aiki da hankali wajen ganin muntsara gudanar da lokutan mu ta hanyoyin da zasu amfanar ko ma samu Allah ya yarda damu sannan tarihin mu ya zama abin alfahari ga zuri’ar da zamu tafi mu bari a wannan duniya. Allah yasa mu dace, amen.

Kawu Sule Rano Malami ne a Jami’ar Bayero da ke Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan