Sanata Malam Shekarau Ya Kaiwa Aminu Dantata Ziyara

330

A daren jiya ne sanatan Kano ta tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya kaiwa fitaccen attajirin nan da ke wato Alhaji Aminu Dantata ziyara a gidansa da ke unguwar Koki a birnin Kano.

Tun da farko dai Sanatan ya wallafa hotunan ziyarar ne a shafinsa na fasebuk, tare da bayyana godiyarsa akan tarbar da attajirin yayi masa.

Sai dai kuma a ɓangare guda masu sharhi akan siyasar Kano sun bayyana cewa har kawo Sanata Malam Shekarau da Attajiri Aminu Dantata ba su ce uffan akan dambarwar da ke tsakanin gwamnatin jihar Kano da kuma masarautar Kano, wanda hakan ya jawo raba masarautar Kano zuwa gida biyar.

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan