Tattalin Arzikin Ƙasar Nan Ka Iya Haɓɓaka Sakamakon Rikicin Iran Da Amurka – Masana

179


A dai dai lokacin da kasar Iran ta sha alwashin daukar fansar harin da Amurka ta kai ta sama, da ya hallaka babban kwamandan zaratan sojojin juyin juya hali na Iran, Qassem Soleimani, manazarta na ganin zai iya shafar dukkan yankin gabas ta tsakiya, da ma wasu kasashen duniya.

Farfesa Bello Muhammad Bada, malami a jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sokoto, kuma mai sharhi akan al’amura, ya bayyana yadda lamarin zai shafi kasashen Africa musamman Najeriya mai arzikin man fetur, a bangaren tattalin arziki.

A cewar Farfesa Bello, ƙasar nan ta dade ba ta samu kudin shiga ba kamar wanda ta samu lokacin yakin Iraqi, saboda haka ake ganin idan wani tashin hankali ya faru tabbas farashin mai zai tashi, inda kasashen da ke fitar da Mai kamar kasar nan zasu kara samun kudin shiga.

Sai dai a bangare guda kuma, bayan karin kudin shigar da kasar nan za ta samu, za ta sayo tataccen mai wanda sai ta biya sama da abin da take biya a baya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan