Ya Mata Su Rika Bincike Kafin Su Yi Aure – Rukayya Dawayya

367

Fitacciyar jarumar masana’antar Kannywood Rukayya Umar Santa, wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya, ta shawarci mata da ke shirin yin aure da su rika yin bincike kafin su tsunduma cikin harkar ta aure.

Jarumar wacce ta samo sunan “Dawayya” daga wani fitaccen fim dinta “Dawayya,” ta ce a lokuta da dama, matan da suka dade ba su samu miji ba, kan yi aure ba tare da sun gudanar da kwakkwaran bincike ba.

“Matsalolin da suka fi damun mu, su ne ta yawan mutuwar aure da kuma yin aure babu bincike.”

Ta kuma kara da cewa, “muna da manyan ‘yan mata da suka dade ba su yi aure ba, wasu sa’aninsu ma sun kusa aurar da ‘ya’ya, to wannan abin yana sa kowa ya zo miki sai ki yi aure.”

“Wannan ita matsalar da ke damun mu, shi ya sa muka dauki wannan bangare, a matsayina na mace.”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan