Kwamandan Hukumar Hana Fasa Ƙwauri na jihar Kwara, Mohammed Uba Garba ya ce Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakin rufe bakin iyakokinta ne don ta inganta tattalin arziƙin Najeriya, ba don ta cutar da ‘yan Najeriya ba.
Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Jami’inta na Huɗɗa da Jama’a, Z. Chado ya aiko wa Labarai24.
“A ranar 20 ga Agusta, 2020, Hukumar Fasa Ƙwauri ta Najeriya ta rufe bakin iyajoki don bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar nan, kuma don maƙobtan ƙasashe su bi Dokokin ECOWAS.
Mista Gaba ya bayyana haka ne kwanan nan lokacin da ya karɓi baƙuncin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Onorabul Salihu Yakubu Danladi, wanda ya kai masa ziyarar girmamawa a ofishinsa.
Mista Garba ya yaba wa Kakakin Majalisar bisa zuwa don sama wa al’ummarsa mafita, yana mai bayyana shi a matsayin babban shugaba, wanda ya damu da matsalolin jama’arsa.
A ta bakinsa, ba an kulle bakin iyakokin ba ne don a yi wa wani kasuwanci da doka ta amince da shi ko kuma wata al’umma bita-da-ƙulli ko kawo tazgaro ba, amma an yi haka ne don a hana fitar da albarkatun man fetur ba bisa ka’ida ba, a ƙarfafa wa manoman gida gwiwa, a yi maganin shigo da makamai da albarusai, muggan ƙwayoyi da ma duka kayayyakin da aka haramta shigowa da su, kuma a ba maƙobtan ƙasashe damar bin Dokokin ECOWAS.
“Kwanturolan, wanda aka turo shi daga Rundunar Yanki ta Seme zuwa Yanki na 3 ya ce Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Najeriya mai aiwatar da manufofin Gwamnatin Tarayya ce kawai, ya kuma bada shawarar cewa ya kamata gwamnatocin jihohi su shigar da ƙorafe-ƙorafensu inda ya dace”, in ji sanarwar.
Ya ce zai ziyarci garuruwan da suke kan iyakoki a jihar don ya haɗu da mutanen da ke yin kasuwanci da doka ta aminta da shi, ba kuma zai sassauta ba bisa ƙoƙarin rundunar na raba yankunan da baƙin haure da laifukan da ake yi tsakanin kan iyaka da kan iyaka.
Mista Garba ya ce Hukumar Hana Fasa Ƙwauri za ta ci gaba da yin dukkan mai yiwuwa don hana shigo da manya da ƙananan makamai, hana fitar da albarkatun man fetur ba bisa ka’ida ba, hana safarar ɗan Adam, hana safarar muggan ƙwayoyi, hana ta’addanci da sauransu.
Sanarwar ta ƙara da cewa Kakakin Majalisar, wanda ya samu rakiyar Shugaban Kwamitin Ilimi da Gina Ɗan Adam na Majalisar, Onorabul Mohammed Baba Salihu, ya bayyana damuwa bisa irin wahalar da ƙauyuka huɗu na ƙaramar hukumar Baruten ta jihar ke fuskanta sakamakon rashin man fetur.
Kakakin Majalisar, wanda ya ce rufe bakin iyakar ya jefa al’ummar yankin cikin matsananciyar wahala, ya yi kira ga Shugaban Rundunar da ya ƙara duba matakin hana kai man fetur kilomita 20 kafin garuruwan dake kusa da bakin iyakoki.
“A halin yanzu, ana siyar da litar man fetur tsakanin N250 zuwa N300”, Kakakin Majalisar ya nuna rashin jin daɗi.
[…] Muƙalar Da Ta GabataBa An Rufe Boda Ba Ne Don A Cutar Da ‘Yan Najeriya- Kwastam […]