Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki, DisCos sun ce za su fara karɓar sabon kuɗin wutar lantarki ne daga 1 ga Afrilu.
Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya, NERC, ta yi ƙarin haske game da lokacin da ƙarin kuɗin wutar lantarki zai fara aiki.
Hukumar ta ce ƙarin kuɗin wutar lantarkin ba zai fara aiki ba har sai ranar 1 ga Afrilu, za a kuma a fara amfani da ƙarin gadan-gadan zuwa ƙarshen 2021.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin don yin ƙarin haske game da ƙarin kuɗin wutar lantarkin, Sunday Oduntan, Babban Daraktan Bincike da Wayar da Kan Jama’a na Ƙungiyar Masu Rarraba Wutar Lantarki, ANED, wata ƙungiya dake ƙarƙashin Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki na Ƙasa, DisCos, ya bayyana ƙarin a matsayin “ƙari kaɗan”.
“Kuɗin wutar zai ci da kasancewa yadda yake a halin yanzu (wato matakan shekara ta 2015) har zuwa 1 ga Afrilu, 2020 lokacin da za a samu ƙari kaɗan don magance ƙarancin kuɗin wutar lantarki, wanda kuma da sannu za a mayar wa mai amfani da wutar lantarki shi har a kammala wannan a ƙarshen 2021”, in ji Mista Oduntan.
“Duba da wannan, muna jaddada cewa ba wani sauyi ko ƙari da za a samu a kuɗin wutar lantarki da ake karɓa yanzu har sai ranar 1 ga Afrilu, 2020 lokacin da sabon ƙarin zai fara aiki a kan tattalin arziƙinmu.
“Muna fatan cewa wannan sanarwa ta fito da matsayinmu, ta kuma kawar da duk wani tsoro ko damuwa da abokan cinikinmu za su samu”, in ji shi.
[…] Muƙalar Da Ta GabataGwamnatin Tarayya Ta Yi Ƙarin Haske Game Da Ƙarin Kuɗin Wutar Lantarki […]