Jami’an Tsaro Sun Lakaɗawa Ƴan Hisbah Duka Tare Da Ƙwace Musu Mota

679

Jami’an tsaro a filin tashi da saukar jirage na Mallam Aminu Kano da ke birnin Kano sun tsare motar babban kwamandan rundunar Hisbah na jihar Kano Sheikh Muhammad Ibn-Sina, bayan sun zane wasu dakarun Hisbar guda biyu.

Wannan al’amari ya faru ne sakamakon dugunzuma jami’an tsaron hukula da filayen jirgn sama na kasa (FAAN) da ƴan hisabar su ka yi a lokacin da suka je filin jirgin saman domin dauko babban kwamandan hisbar.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaron filin jirgin sun yi wa dakarun Hibah biyu taron dangi tare da kulle su bayan sun zane su yayin da suke cikin kakinsu na ‘yan Hisbah.

Tun da farko an samu sabani tsakanin jami’an tsaron filin jirgin saman da kuma jami’an Hisbah akan wurin ajiye motar Ibn-Sina a filin jirgin saman.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa rai ya baci ne sakamakon kin biyayyar da hadiman Ibn-Sina suka yi yayin da jami’an FAAN suka umarcesu da su ajiye motar shugaban nasu a wurin ajiye motoci na kudi, amma suka ki.

Tirjewar jami’an Hisbah ta jawo cacar baki mai zafi a tsakaninsu da jami’an FAAN’ lamarin da ya kai har an bawa hammata iska, a cewar majiyar.

Dakarun Hisbah sun isa filin jirgin saman ne domin dauko shugabansu wanda jirginsa zai sauka da misalin karfe 2:00 na rana.

Sai dai, kokarin manema labarai na jin ta bakin mahukuntan filin jirgin sama ya ci tura, kasancewar sun ki yin magana da wakilan jaridu.

Lawan Ibrahim, kakakin rundunar Hisbah, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da daukan alkawarin bayar da cikakken bayani a nan gaba.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan