Real Madrid Na Neman Lingard Na Manchester

79

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid itama idonta ya makance wajen neman dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United kuma dan asalin kasar Ingila wato Jese Lingard.

Inda daman tuni wasu kungiyoyin kwallon kafan suke nuna sha’awarsu ta daukan wannan dan wasa to itama Real Madrid tashiga sahu.

Shidai Jese Lingard shekarar sa 1 cif a Manchester United baici kwallo ba sannan kuma bai taimaka anci kwallo ba.

Shin kome Real Madrid suke nufi game da neman Lingard wanda akwai ‘yan wasa matasa masu gasa da junansu a kungiyar ta Madrid kuma Lingard yaje alhalin ko a Manchester United baya iya cin kwallaye yadda ya kamata?

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan