Ƙasar Iran Ta Kaiwa Sojojin Amurka Mummunan Hari A Iraqi

293

Kasar Iran ta kaiwa sansanin sojojin Amurka mummunan hari a kasar Iraqi ta hanyar amfani da makami mai linzami.

Harin wanda aka kai shi a yau Larabar nan, wata majiya ta sanarwa da kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an harba makamai masu linzami har guda tara akan sansanin sojojin na kasar Iraqi mai Ain Al-Asad, wanda yake shine sansani mafi girma da sojojin kasashen waje ke zaune a kasar.

Harin an kawo shi ta bangarori uku ne da tsakar daren Larabar, in ji majiyar.

Wannan shine karo na farko da kasar Iran din ta dauki alhakin kai hari sansanin sojojin, inda ta bayyana hakan a wani gidan talabijin na kasar.

Wannan shine kusan karo na 15 da sansanin sojojin Amurka suka fuskanci hari na makami mai linzami a yankin kasar Iraq din, amma duka babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai hare-haren.

Wannan hari dai yazo ne bayan harin da kasar Amurka ta kaiwa filin jirgin sama na birnin Baghdad, wanda yayi sanadiyyar mutuwar babban kwamandan sojojin kasar, Janar Qasem Soleimani.

Mataimakin Sakatare na hukumar tsaron Amurka, Jonathan Hoffman, a wata sanarwa ya bayyana cewa “Da misalin karfe 5:30 na yamma a ranar 7 ga watan Janairu, kasar Iran ta harbawa sojojin Amurka makamai masu linzami masu yawan gaske.”

“Tabbas wadannan makamai an harbo su daga kasar Iran ne kuma an kai harin kan sansanin sojojin Amurka guda biyu dake kasar Iraqi,” in ji Hoffman.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan