BUK Ta Karrama Farfesa Baturiya Da Ta Shafe Shekara 50 Tana Koyar Da Hausa

143

Jami’ar Bayero ta Kano, BUK, ta shirya wani taro na ƙasa da ƙasa kan nazarin Hausa don karrama wata malama ‘yar ƙasar Poland, Nina Pawlak, wadda ta shafe shekaru 50 tana bincike a harshen Hausa da sauran harasan Afirka.

Majiyarmu ta ruwaito cewa Miss Pawlak, Farfasar Harasa a Jami’ar Warsaw ta Poland, ta duba kundin Digiri na uku na malaman BUK, Hafizu Miko Yakasai da Isah Yusuf Chamo, kuma ta yi aiki a matsayin jami’ar jarrabawa ta waje ga Yakubu Magaji Azare da kuma wani farfesan BUK.

Taron na kwana biyu wanda aka fara ranar Talata, Cibiyar Binciken Harsunan Najeriya, Fassara da Hikimomin Al’umma ce ta shirya shi, bisa haɗin gwiwa da Sashin Harsunan Najeriya da Sashin Nazarin Harasa da Harsunan Ƙasashen Ƙetare.

Da yake buɗe taron, Shugaban Jami’ar, Muhammad Yahuza Bello ya bayyana Miss Pawlak a matsayin gogaggiyar malama, wadda ta sadaukar da rayuwarta ga nazari da koyar da Hausa.

Mista Bello, Farfesan Ilimin Lissafi, ya bayyana godiyar BUK ga Miss Pawlak bisa wannan gudunmawa ta tsawon rayuwa.

“Ina ji daɗin gabatar da godiyar wannan jami’a bisa gudunmawarki mara iyaka, bisa yawan malamanmu da kika ba horo, kika duba aikinsu, kika ba su maki kuma kika tallafa musu, bisa haɗin kai da kika raina, kuma kika sa ya ɗore, bisa littattafai da wallafe-wallafe da muka yi musaya, da kuma ɗaukar nauyi da ziyarce-ziyarce.

“Ina kuma gabatar muku da godiyar ɗalibanmu da malamai bisa ilimin da kika bayar, da kuma godiyar al’ummarmu bisa aikin da kika yi don ajiye harshenmu da al’adarmu a kan saiti, tana raye, lafiya lau kuma tana tasowa.

Da take mayar da martani, Miss Pawlak ta ce ta sadaukar da rayuwarta ta karantarwa ne wajen nazarin harshen Hausa a matsayin wata hanyar bunƙasa fahimta tsakanin ƙasashen Afirka da na Turai.

“Bayan na bar aiki, ina da nufin rubuta ƙamusun Hausa da Polish don masu koyon Harshen Hausa a Poland, ƙasata”, in ji ta.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan