Garken Birarruka Sun Hana Manoman Wata Jiha Sakat

174

Yawan birrai da ke addabar jama’a a jihar Himachal Pradesh da ke arewacin India, ya sa al’umar yankin sun kauracewa gonakinsu saboda barazanar da amfanin gonakinsu ke fuskanta.

Aikace-aikacen bil adama da suka hada da rage dazuka da bunkasar birane, sun sa dabbobin suna kai hari kan gonaki don neman abinci, suna kuma lalata amfanin gonaki da darajarsu ta kai ta miliyoyin daloli.

Masana harkar noma suna koya wa manoma dabarun yadda za su shawo kan wannan matsalar.

Anjana Pasricha ta ce yankin Magroo na cikin garuruwan da ke yankin Himalayan da ya amfana da ire-iren wadannan shawarwarin.

Kamar yadda manomi, Babu Ram a kauyen Magroo ya ce, “da rana muna zagayawa da karnuka, muna kuma amfani da bindiga ta iska.

Hakan a cewar shi, na sa birran suna tserewa, in ba haka ba yana da wahala a kau da su.”

Suna koyan cewa shuka ganye maimakon abubuwan gargajiya kamar shinkafa na da amfani.

Bincike ya yi nuni da cewa, birrai ba sa kai hari ga amfanin gona kamar icen Aloe vera, wata shuka da ke magani da ita.

Daraktan Yankin arewacin India na wani kwamitin kula da harkokin tsirran da ake magani da su, Arun Chandan, ya ce suna koya wa manoma irin nau’in amfanin gonar da za su iya shukawa gwargwadon kasa da ruwan da yankin da gonakinsu suke

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan