- Iran ta nuna qarfinta a aikace, domin ta yi alqwarin kai wa Amurka hari don ramuwar gayya, kuma ta tabbatar da hakan a cikin kwana hudu tal da kashe mata Janaral, kuma a daidai sa’ar da aka kashe shin (1:20 na dare). Shin wannan zallar qarfin ikon Iran ne ko kuwa kamalar cika alkawari ne nata koda kuwa ba ta da qarfin? Duka ne.
- Tsakanin inda Iran ta cilla rocket dinta zuwa sansanoni biyu na sojin Amurka da rocket din suka dira a ciki, tafiyar mil dubu guda ne, kimanin kilomita 1600. Wato nisan tafiyar da ta kai tsawon zuwa da dawowa daga Kano zuwa Legas. Yaya aka yi Iran ta cilla rocket har guda 30 a irin wannan nisan tafiya amma radar Amurka da ake kurantawa ba ta iya hangowa bare ta sa a tare ko da rocket guda daya ba? Shin fasahar Iran ce ta fi qarfin ta Amurka ko kuwa kururutawar da aka yi wa fasahar Amurkar dama farfagandar iska ce kawai? Wannan manazarci yana ganin sa hannun Allah ne. A tuna da ayar nan ta “wa maa ramaita iz ramaita walaa kinnallaaha ramaa.”
- Amurka ta ce a take za ta maida martani. Amma har zuwa kimanin awa goma sha daya bayan harin, babu alama. Yanzu ma cewa take yi tana nazarin hasarorin rayuka da barnar dukiyar da harin ya yi ne. Shin me hakan ke nufi? Amurka ta san Iran ba kanwar lasa ba ce sabanin qarerayin da Wahabiyawa suke yawo da shi a nan social media. Iran ta ce idan Amurka ta kai mata hari, to, za ta aika da harinta cikin qasar Amurkar, abin da ba a taba tunanin yi ba a tarihin duniya. Manazarcin nan ya zagaya akasarin kafafen yada labaran Turai, amma bai ga inda aka musa cewa Iran din ba za ta iya kai harin cikin Amurka ba har zuwa yanzu. Shin wannan qarfi mai izza, daga ina Iran ta same shi? Mai rubutu na cewa daga Allah ne kawai. Wato a cikin bin Allah ta samu. A tuna da ayar: “Walillaahil izzatu wa li-rasuulihi wa lil mu’uminin…”
- Iran ta nuna tarbiyyar Musuluncin da ta koya daga Iyalan Gidan Manzon Allah (sawa). Tun kafin ta kai harin, dama ta ce ba za ta kashe fararen hula da wadanda ba su ji ba ba su gani ba. A kan sojojin Amurka kawai za ta kai harin. Su ma sojojin, sai ta bayyana ashe iya wadanda ke sansanonin Iraqi ne kawai, wato muhallin da aka yi amfani da su wurin kashe mata Janaral. Wannan abin alfahari ne ga kowane Musulmi da ke duniya hususan ‘yan Shi’a, domin Iran ta nuna a aikace cewa, Musulunci ba addinin ta’addanci ba ne. Kuma ba ya wuce iyaka wurin ramuko.
- Yadda kafafen yada labarai suka ruwaito guje-gujen da sojojin qawance ke yi daga Iraqi, ya qara tsaraita Amurka da barinta tilo a wannan hari na Iran wanda Amurkar ba ta san inda ya dosa ba in har girman kai ya sa ta cigaba da shi. Wala’alla hakan ya bude baqon sabon shafi a siyasar yaqin da Amurka ta saba yi na tattaro sojojin qawance don su tayata, maimakon ta yi yaqinta ita kadai.
- Daukakar da Janar Qassem Suleimani ya samu tare da girmamar matsayinsa wadanda suka sa qasa irin Iran mai kauda kai da yawan yafiya ta himmatu wurin daukar fansa a kan kashe shi kawai, izna ce ga masu taqaitaccen tunani. Domin hakan ya nuna miraran cewa ba ka buqatar zama malami ko zama dan wani babban gida kafin ka samu babban matsayi da karbuwa. Himmarka, tawali’unka, haqurinka da ikhlasinka a dukkan aikin alherin da kake yi zai kai ka ga matsayin da ba ka taba mafarkinsa ba a duniya ko a lahira ko ma duka biyun kamar dai shi shahidin marigayin.
- Zuwa yanzu ta bayyana cewa qarfin soja, fasahar technology da ilmukan kimiyya, ba dole sai a Turai ake samunsu ba, kuma ba dole sai da Turanci, Faransanci, Chinanci ake gane su ba. Da harshenku na gida za ku iya isa ga kowane matsayi. Ku dai ku zama masu himma kuma masu gaskiya kawai.
Muhammad Bin Ibrahim ya rubuto daga Kaduna

Turawa Abokai