Hotunan Obasanjo A Gona Yana Sassabe Sun Haifar Da Muhawara

171

Wasu hotunan tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo a gona yana sassabe tare da sauran wasu mutane da ake ganin makusantansa ne sun haifar da muhawara a tsakankanin al’ummar ƙasar nan.

Tun da farko hotunan sun fara shawagi ne a kafafen sadarwa na zamani, hotunan da su ka nuna hoton Obasanjo a wata gona yana sassabe tare da wasu mutane da ke ganin makusantansa ne

Bayyanar wadannan hotunan sun haifar da muhawara a tsakankanin ma’abota shafukan sada zumunta na zamani. Wasu sun bayyana ra’ayinsu akan daman wannan ba sabon abu bane daman Obasanjo manomi ne, wasu kuma suna kallon hakan a matsayin amsa kiran da gwamnatin Buhari ta ke na a koma noma

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan