Kalmomin Mahaifiyar Abubakar Shekau Game Da Shi

295

Falmata Abubakar mahaifiyar Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ta bayyana wadannan kalmomi akan ɗan na ta

Tun da Shekau ya hadu da Mohammed Yusuf, ban sake ganinshi ba,”

“Ko ya mutu, ko yana nan da ransa ne, ba ni da masaniya. Allah kadai ya sani. Shekaru na goma sha biyar kenan tun da ganinsa,”

“Na san dana ne, kuma kowa ya san son da uwa ke wa danta, amma halayenmu sun sha banban,” inji ta. “Ya jefa mutane da dama cikin bala’i. Ina ma zan ganshi domin in ja hankalinsa? Ya jefa jama’a da dama cikin tashin hankali, amma ina rokon Allah ya shiryeshi.”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan