Tarihin Mai Martaba Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero

  189

  An haifi mai martaba Sarkin Alhaji Aminu Ado Bayero a shekarar 1961, shi ne ɗa na biyu a jerin ƴaƴan mai martaba Sarkin Kano Ado Bayero. Ya fara da karatun alkur’ani mai girma kamar yadda yake bisa tsarin tarbiyyar ƙasar Hausa.

  Bayan ya samu ilimin addinin Islama, mai martaba Sarkin Bichi ya fara karatunsa na Furamare a Kofar Kudu da ke gidan mahaifinsa, bayan kammala karatun Furamare ya samu nasarar shiga Kwalejin Birnin Kudu a jihar Jigawa.

  Bayan kammala Kwalejin Birnin Kudu cikin nasara wacce hakan ce ta bashi damar wucewa zuwa jami’ar Bayero da ke Kano, inda ya samu damar karanta aikin jarida wato Mass Communication a matakin digiri.

  Mai marraba Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero ya yi hidimar ƙasa a gidan talabishin na ƙasa da ke birnin Makurdi a jihar Beneu wato NTA Benue.

  Bayan Kammala hidimar ƙasa mai martaba Sarkin Bichi ya fara aiki da kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na KABO AIR a matsayin jami’in hulɗa da jama’a na wannan kamfanin.

  Irin ƙwazo da himma da mai martaba Sarkin Bichi ya ke da shi, hakan ya bashi damar komawa kwalejin koyon tuƙin jirgin sama da ke garin Oakland a jihar California ta ƙasar Amurka.

  Bayan ya samu ƙwarewa daga wannan kwaleji ta koyar tuƙin jirgin sama, hakan ya sanya zama ƙwararren matuƙin jirgin sama a kamfanin KABO AIR.

  A Shekarar 1990 ne mahaifinsa mai martaba Sarkin Kano marigayi Alhaji Dakta Ado Bayero ya fara naɗa shi a hakimci, inda ya dace da sarautar Ɗan Majen Kano hakimin Dala, bayan wasu ƴan watanni sai mai martaba Sarkin Kano ya ciyar da shi gaba zuwa Ɗan Buram ɗin Kano.

  A shekarar 1992 mai martaba Sarkin Bichi ya zama Turakin Kano hakimin Dala.

  Duba da irin ƙwazonsa tare da rikon amanarsa, a shekarar 2000 masarautar Kano ta naɗashi Sarkin Dawakin Tsakar Gida hakimin Dala.

  A cikin shekarar 2014 mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ɗaga likkafar mai martaba Sarkin Bichi zuwa Wamban Kano hakimin Birni da Kewaye.

  A ranar 10 ga watan Mayun shekarar 2019 ne majalisar dokokin jihar Kano ta samar da dokar da ta amince da ƙirƙirar masarautun Bichi da Rano da Ƙaraye da kuma Gaya, inda Alhaji Aminu Ado Bayero ya zama cikakken Sarkin Bichi Mai daraja ta ɗaya

  Mai martaba Sarkin Bichi yana matan aure da ƴaƴa

  Turawa Abokai

  1 Sako

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan