Wani Fusataccen Uba Ya Canzawa Ɗansa Suna Daga Buhari Zuwa Kwankwaso

96

A wani al’amari mai kama da almara, domin kuwa wani magidanci ne mai suna Salisu Matagwa ɗan kimanin shekaru 45 mazaunin unguwar Kumbiya-Kumbiya a jihar Gombe, ya tara ƴan uwa da abokan arziƙi domin bikin sauyawa ɗansa mai shekaru 9 da haihuwa suna daga Muhammadu Buhari zuwa Rabi’u Kwankwaso.

Wannan magidanci ya sake yankawa wannan yaro ragon suna tare da shirya ƙwarya-ƙwayar liyafar bikin sake raɗin sunan wanda ya samu halartar ƴan uwa da abokan arziƙi. Ya kuma ce ya ɗauki wannan matakin canza sunan ne saboda tseratar da yaron daga tsangwamar mutane tare da cin zarafi, saboda a zatonsu sunan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari aka saka masa.

Salisu Matagwa ya ƙara da cewa tun asali ɗan na sa ya ci sunan kakakin majalisar dokoki na ƙasa Salisu Buhari, amma kuma mutane suna kuskuren zaton cewa an saka masa sunan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne, wanda har ana yi masa laƙabi da janar Buhari kuma hakan yana ci masa tuwo a ƙwarya.

Hakazalika ya bayyana takaicinsa akan yadda shugaba Muhammadu Buhari ya kasa taɓukawa al’ummar ƙasar nan komai, wanda hakan ya sanya a kullum farin jininsa ya ke ƙara raguwa a tsakankanin alummar ƙasar nan.

Ya ƙara da cewa tun da al’ummar ƙasar nan ba su da kyakykyawan nufi akan shugaba Buhari hakan ya sanya ya canzawa ɗansa suna zuwa Rabi’u Kwankwaso wanda a halin yanzu ya fi Buhari farin jini da karbuwa a tsakankanin al’ummar ƙasar nan.

A ƙarshe ya ce bai san Rabi’u Kwankwaso ba, balle har wani ya yi zaton ko yanl bashi wani abu ne da har ya canzawa ɗan sa suna zuwa sunasa. Ya ce ya yi haka ne domin ganin damarsa kawai.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan