Ayau za a fara fafata gasar Super Cup ta kasar Andalos tsakanin kungiyoyin Kwallon kafa guda 4 dasuka karkare a saman teburin gasar ajin Laliga ta 2018 zuwa 2019 inda Barcelona ta zamo zakara.
Za a fafata wasannin a kasar Saudiyya inda za a fara gasar ayau Laraba.
Saidai gasar ta bana tazo da sabon salo inda a shekarun baya ana fafata wannan wasa tsakanin kungiyar kwallon kafan data lashe gasar Laliga da kuma wadda ta lashe gasar Copa del Rey.
Ayau Larabar dai za a fafata wasan farko tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Valencia da Real Madrid da misalin karfe 8:00 na dare agogon Najeriya.
Saikuma gobe Alhamis za a fafata tsakanin Athletico Madrid da Barcelona.
Acikin kungiyoyin kwallon kafar nan guda 4 za a samu wadda zata zamo zakara akarshen gasar.