Yadda Gwamnan Bayelsa Yahana Bayelsa Queens Miliyan 22

171

Tun bayan da kungiyar kwallon kafan mata ta Bayelsa Queens dake jahar Bayelsa ta lashe gasar cin kofin ajin Premier ta kasar nan ta bangaren mata ta 2018 zuwa 2019 gwamnatin jahar tayimusu alkairin cewa ta basu kyautar kudi har naira miliyan 22.

Inda tun a watan Janairu na 2019 akayimusu wannan alkairi yau shekara guda kenan amma har yau gwamnatin jahar ta gaza cika wannan alkawari.

Jaridar Labarai24 ta tuntubi wasu masu ruwa da tsaki na gwamnatin ta Bayelsa musamman mai magana da yawun gwamnan dangane da wannan batu sai yace ” Tabbas gwamnan Bayelsa yayimusu wannan alkawari kuma anrubuta cewar abiyasu kudin amma matsalar da aka samu amma sashen al’amuran kudi na jahar ne basu bayar da wannan kudi ba”

Haka ba iya alkawarin kudi gwamnan yayiba harma da alkawarin sabuwar mota doguwa domin amfani da ita wajen zuwa sassan jahoshin nan buga wasanni, amma haryanzu motoci tsofaffi Bayelsa Queens din suke hawa.

Aranar 28 ga watan Janairunnan gwamna Dickson zaiyi murnar bikin zagayowar ranar haihuwarsa inda kungiyar kwallon kafan ta Bayelsa Queens tayi fatan zaiyi amfani da wannan dama domin biyansu kudinsu.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan