Za’a Harbe Raƙuma 10,000 A Australia Saboda Barazanar Shanye Ruwa

1031

A ƙalla kimanin raƙuma 10,000 ne su ke gaf da rasa rayukansa a yankin da ake fama da matsanancin fari a kasar Australia, sakamakon korafin da mazauna yankin su ka yi akan yadda raƙuman su ke kokarin shanye ruwan da ya ke yankin.

Wani jami’i a yankin karamar hukumar Anangu Pitjantjatjara Yankunytjatjara ya bayyana cewa dubban garken rakuma tare da sauran jinsin wasu dabbobi ne su ka cika wannan yanki, kuma suna shiga saƙo da lungu domin neman ruwan sha wanda hakan ya jefa alummar cikin mawuyacin hali

Ya ƙara da cewa taruwar wannan garken raƙuman a wannan yankin da yake faƙo ne, hakan zai jefa al’ummar wannan yanki cikin ƙarancin ababen more rayuwa, saboda haka ya zama dole a taƙaita yawan raƙuman.

A bisa neman ruwan sha da raƙuman su ke yi su kan shiga gidajen mutane da duk wani guri da su ke ganin za su samu ruwan sha. A wasu lokutan kuma akan samu gawarwakin raƙuman masu yawa a wannan yanki.

Mahukunta a wannan yanki dai za su yi amfani da ƙwararru akan harbin bindiga da za su harbe waɗannan raƙuma ta hanyar amfani da jirgi mai saukar ungulu.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa akwai kimanin adadin raƙuma sama da miliyan ɗaya a ƙasar Australia, kuma a kullum ana ƙara samun adadin yawan raƙuma a ƙasar

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan