Ɗalibin Kwankwasiyya Ya Ɗauki Nauyin Karatun Ɗalibai 150 A Kano

261

Wani da ya amfana da Shirin Tallafin Karatu na Kwankwasiyya, Ibrahim Garba, ya ɗauki nauyin karatun fiye da ɗalibai 150 ‘yan asalin jihar Kano don su yi karatu a manyan makarantu daban-daban na jihar da ma na sauran sassan Najeriya.

Majiyarmu ta bada rahoton cewa Mista Garba yana ɗaya daga cikin ɗalibai 501 da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso a jihar ɗauki nauyinsu zuwa Malaysia don yin Digiri na Uku a ‘Strategic Business Management’.

A halin yanzu, Mista Garba yana koyarwa a Sashin Nazarin Kasuwanci na Jami’ar Bayero ta Kano, BUK.

Wani ma’abocin amfani da shafin Twitter, Abdullahi Ibrahim ne ya bayyana haka a shafinsa mai suna @Kwankwason_tuwita, inda ya jiyo Mista Garba yana cewa ya ɗauki matakin ɗaukar nauyin karatun ne don rage yawan ɗaliban da ba sa zuwa makaranta a jihar Kano.

Mista Garba ya bayyana cewa shirin ya fara da ɗalibai 15 a 2019, kawo yanzu kuma, an ɗauki nauyin ɗalibai 30 da za su yi karatu a kwasa-kwasai daban-daban a jami’o’in dake Kano da sauran maƙobtan jihohi.

A ta bakinsa, an shigar da yara 40 makarantun Islamiyya, an kuma shigar da yara fiye da 65 makarantun firamare da sakandire a ƙarƙashin wannan shiri.

“Yawanci mukan nemi ɗalibai da suke da kyakkyawan sakamako a Jarrabawarsu ta Kammala Sakandire, SSCE, daga nan sai mu sai musu fama-famai daga hukumar JAMB.

“Waɗanda suka iya samun makin da ake buƙata don samun gurbin karatu daga cikinsu, mukan yi fafatukar sama musu guraben karatu a makarantun da suke so, sannan mu ci gaba da ɗaukar nauyinsu har su kammala.

“Bara, mun ɗauki nauyin ɗalibai 15, a bana kuma, mun ɗauki nauyin wasu 15 daga ɗan abinda muke da shi.

“Muna fata wannan adadi zai ci gaba da ƙaruwa. Kuma abin sha’awa, ban ma san wasu daga cikin yaran nan ba ko iyayensu. Ƙa’idojin da aka sa kawai su ne cancanta da ƙwazo.

“Tuni na sauya wannan shiri ya zama gidauniya, wadda na kira ta da Gidauniyar IG Muhammad (an sa mata suna na) don ɗaukar nauyin karatun ɗalibai a ƙaramar hukumar Tarauni”, Mista Garba ya bayyana haka.

Yayinda yake alƙawarin ci gaba da wannan shiri don kai shi inda ma bai kai ba, Mista Garba ya bayyana cewa mafarkin da yake da shi shi ne ya ɗauki nauyin karatun marasa galihu zuwa ƙasashen waje, kamar yadda Kwankwaso ya ɗauki nauyinsa.

Saboda haka sai ya gode wa tsohon gwamnan bisa ƙirkiro da wannan shiri, inda ya yi kira a gare shi da ya ci gaba da haka har sai an kakkaɓe jahilci kwata-kwata a jihar.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan