A jihar Massachusetts ta Amurka an zabi mace Musulma ta farko ‘yar asalin Pakistan Sumbul Siddiqui a matsayin shugabar karamar hukuma.
Labaran da jaridun kasar suka fitar sun ce an zabi Sumbul Siddiqui mai shekaru 31 a matsayin Shugabar wata karamar hukuma dake garin Cambridge na jihar ta Massachusetts.
Sumbul Siddiqui tare da iyalanta sun koma Amurka da zama a lokacin tana da shekaru 2 da haihuwa.

Turawa Abokai