An Samu Mutum Na Biyu A Duniya Da Ya Warke Daga Cutar Ƙanjamau

372

Wani da ke dauke da kwayar cutar HIV a Birtaniya ya zama mutum na biyu da aka sani a fadin duniya da aka tabbatar da cewa ya rabu da cutar dake karya garkuwar jiki.

A wani taro da akayi a birnin Seattle dake Amurka, cibiyar majalisar dinkin duniya da ke jan ragamar kokarin da ake yi na kawar da cutar ta HIV a duniya ta ce, cibiyar ta sami kwarin gwiwa akan yiwuwar warkar da wani mai cutar HIV, amma har yanzu akwai sauran aiki.

Masana a fannin kimiyya sun kai kusan shekaru 40 suna neman maganin cutar HIV/ AIDs dake karya garkuwar jiki, wadda kuma ake kira Sida. Daraktan cibiyar kula da HIV ta majalisar dinkin duniya da ake kira UNAIDS a takaice, ya bayyana cewa wani mutum a birnin London ya rabu da cutar HIV a abinda ya kira “babbar nasara.”

Stephane Dujarric, mai magana da yawun babban sakataren majalisar dinkin duniya ya sanar da hakan.

Dujarric ya kara da cewa “Wannan babbar nasara da aka samu ta bamu kwarin gwiwa, amma kuma ya nuna sauran aikin dake gaban mu wajen kawar da cutar HIV ta hanyar kimiyya, da kuma muhimmancin ci gaba da maida hankali akan kokarin dakile kamuwa da cutar da kuma yin jinyar ta.”

Timothy Ray Brown celebrates the 10th anniversary of his Bone Marrow Transplant that appears to have cured his HIV. The celebration was held during an HIV conference at the Crown Plaza Hotel in Seattle, Washington on Feb. 12, 2017.
Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan