BUK Ta Rage Kuɗaɗen Ɗakunan Kwanan Ɗalibai

302

Jami’ar Bayero ta Kano, BUK, ta rage kuɗaɗen ɗakunan kwanan ɗalibai da a baya ta ƙara ga ɗalibai ‘yan Najeriya.

Idan dai za a iya tunawa, Jami’ar Bayero ta ƙara kuɗaɗen ɗakunan kwanan ɗalibai da fiye da kaso 100% a wasu wuraren, kuma ta shigo da wasu sabbin caje-caje na kuɗaɗen gudanarwa.

Wata sanarwa da aka bayar a mujallar jami’ar ta mako-mako ranar Juma’a ta ce an yi ragin ne sakamakon ƙorafe-ƙorafe da Ƙungiyar Ɗalibai ta Jami’ar Bayero ta Kano, SUG ta shigar.

“Hukumar Gudanarwar Jami’ar ta buƙaci Shugaban Kwamitin Majalisar Dattijan Kan Kuɗaɗen Makaranta da Caje-Cajen Kuɗi da ya haɗa kai da Daraktan Sashin Kula da Harkokin Ɗalibai, Daraktan Sashin Tsaro da Darkatan Sashin Jarrabawa’, Bada Guraben Karatu da Adana Bayanai, DEAR don tattaunawa da shugabannin Ƙungiyar Ɗalibai.

“Biyo bayan ganawa da tuntuɓar Hukumar Gudanarwar, an amince cewa za a yi ragi”, in ji sanarwar.

A cewar sanarwar, a yanzu ɗalibai ‘yan Najeriya masu karatun gaba da digiri na farko za su riƙa biyan N20,150 maimakon N25,150 da aka sanar a baya.

Amma, har yanzu ɗaliban ƙasashen waje za su riƙa biyu N80,000 ne kamar yadda aka sanar a baya, ba tare da wani ragi ba.

Sanarwar ta kuma ce an rage wa ɗalibai masu karatun digiri na farko N2,000 kacal.

Haka kuma, matsugunin ɗalibai masu karatun digiri na farko da gado da katifa a yanzu N18,090 ne, yayinda kuma matsuguni ba tare da katifa zai zama N10,090.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan