Hukumar Hizbah a jihar Jigawa ta sanar da cewa ta kashe auren dole guda 330 da aka gudanar a shekarar 2019 bayan amaren sun gudu daga gidajen.
Shugaban hukumar Ustaz Ibrahim Garki, ne ya bayyanawa manema labarai cewa sun kashe auren dolen ne bayan amaren sun kai ƙara ofishohin Hizbah dake jihar. Ya ce bayan kashe auren, hukumar ta mayar da amaren wajen iyayensu.
Hakazalika hukumar ta baiwa iyayen waɗanda aka kashewa auren shawara su sanya zawaran a makaranta, saboda yawancin yan matan da aka kashewa auren dolen kananan yara ne
A ƙarshe ya ce hukumar Hizbar ta samu nasarar dakile wasu auren dolen da aka shirya.



Turawa Abokai
[…] Click to share on Facebook (Opens in new window) […]