Tsananin Yunwa Ya Kashe Fursunoni 17

162

Rahotanni sun tabbatar da cewa wata biyu kenan ba a kai wa gidan yarin Makala da ke birnin Kinshasa abinci ba.


Kungiyoyin sun gano cewa baya ga rashin samar da abincin, ‘yan gidan yarin ba sa samun magani da kuma tsabtataccen muhalli.

Wani ma’aikacin gidan yarin da bai amince da a fadi sunansa ba ya fadawa wakilin BBC cewa babu ranar da ba a mutuwa a gidan kason saboda matsanancin halin da a ka jefa wadanda ake tsaren da su.


Karancin abincin ya sa mutane 8,000 dogaro da ‘yan uwansu da sama musu abin da za su ci.


Haka kuma gidan kason ya cunkushe inda ya ninka yawan ‘yan gidan yari da ya kamata ya dauka har sau biyar.


Babban abinda ya fi damun kungiyoyin shi ne kashi shida cikin dari ne kacal aka yankewa hukunci a gidan yarin, yayin da sauran kashi 94 ke jiran makomar su bayan tuni sun shafe shekaru da dama a tsare.


Sai dai mataimakin ministan harkokin cikin gidan kasar ya fadawa kafafen yada labarai cewa tuni a ka ware kudi don agazawa gidan yarin, kuma bai musanta zargin cewa yunwa ta kashe wasu ba.

Gidauniyar Bill Clinton for Peace ce ta fara gano halin da ake ciki a gidan yarin.


Wannan ba shi ne karon farko ba da yunwa ke kashe ‘yan gidan yari a demokradiyyar Congo, don ko a bara mutane arba’in ne suka mutu a irin wannan matsanancin hali a wani gidan yarin daban.

Rahoton BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan