Abinda Yasa Muka Dakatar Da Amfani Da NIN A UTME Ta 2020- JAMB

246

A ranar Asabar ne Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu, JAMB, ta dakatar da amfani da Lamabar Shaidar Zama Ɗan Ƙasa, NIN a Jarrabawar Bai Ɗaya ta Shiga Manyan Makarantu, UTME ta 2020.

Magatakardar Hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana haka ga manema labarai a yayin wani taron manema labarai a Hedikwatar Hukumar dake Abuja.

Ya ce an yanke hukuncin dakatar da amfani da lamabar ne a matsayin abinda ya zama dole a UTME ta 2020 da Jarrabawar Shiga Aji Biyu na Manyan Makarantu, DE bayan samun kiraye-kirayen dakatar da hakan daga masu ruwa da tsaki.

“Mun kuma yanke shawarar dakatar da hakan a matsayin wani abinda ya zama wajibi sakamakon wasu dalilai na tangarɗar na’ura.

“Jiya muka cimma matsaya, kuma muka yanke shawarar cewa za mu dakatar da amfani da NIN a matsayin mani abu da ya zama wajibi a UTME ta 2020 da DE har sai 2021.

“Zuwa lokacin, zai zama an ba ɗalibai sheƙa ɗaya don su yi rijista.

“Wannan bai shafi ma’aikatanmu na din-din-din da na wucin gadi ba waɗanda za su yi aikin jarrabawar saboda za su buƙaci NIN don tantancewa.

“Mun zagaya mun ga sha’awa da jajircewar ɗalibai; maganar gaskiya ita ce abinda muke so mu cimma ba mai yiwuwa ba ne a halin yanzu, saboda haka ba za mu ɗora wa ɗalibai ƙarin wahala ba”, in ji Mista Oloyede.

Mista Oloyede ya kuma lura da cewa dalilan tangarɗar na’ura da ake da su a ƙasa dangane da tsarin yin rijista a Hukumar Bada Katin Shaidar Zama Ɗan Ƙasa, NIMC yana daga cikin manyan dalilan da suka sa aka dakatar da amfani da lambar.

A ta bakinsa, shirye-shirye na ƙasa don samar da wani tsari mai ci gaba sosai da zai wadatar a yi wannan tsari.

Ya kuma ce JAMB da NIMC za su ci gaba da musayar rahotonnin sirri da kuma tsare-tsare don samar da lambar a nan gaba ba tare da tazgaro ba.

Ya jaddada cewa buƙatar da ta sa aka sa NIN ta zama wani abu na wajibi shi ne a yi maganin masu yin damfarar shaida a lokacin jarrabawar.

Shi ma da yake jawabi, Darakta Janar na NIMC, Aliyu Azeez, ya ce ɗaukar wannan mataki ya zama dole saboda aikin ya yi wa hukumar yawa, yadda aka ɗora mata aikin cikin ƙanƙanin lokaci.

Ya ce NIMC tana da cibiyoyi 1,000 a duk faɗin ƙasar nan waɗanda za ta iya yin aikin da su, kuma tana buƙatar cibiyoyi 4,000 don gudanar da wannan aiki.

Amma, ya bayyana cewa za su ci gaba da haɗa gwiwa da JAMB, yana mai shawartar iyaye da ɗalibai da za su yi jarrabawa a 2021 da su yi amfani da wannan dama don samun lambar a cikin lokacin da aka ƙayyade don gudun yin abubuwa a makare.

Mista Azeez ya kuma ce zuwa 2021, za a riƙa yin rijistar NIMC a Cibiyoyin Ɗaukar Jarrabawa ta Kwamfuta na JAMB, CBTCs, a dukkan faɗin ƙasar nan, inda za a ajiye ma’aikata don ɗaukar bayanan ɗalibai.

A kwanakin baya ne dai Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ya bada rahoton cewa dukkan ɗalibai da za su yi UTME da DE a bana sai sun samu lambar NIN kafin su iya ɗaukar jarrabawar da JAMB ke shiryawa.

Za a fara rijistar UTME da DE ranar Litinin, 13 ga Janairu, za kuma a kammala ranar 17 ga Fabrairu.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan