Dabo Babes Ta Lashe Gasar Tofa Premier Ta Kano

267

Kungiyar kwallon kafa ta Dabo Babes ta lashe gasar Tofa Premier ta jahar Kano da aka kammala.

Dabo Babes din ta lashe gasar ne bayan ta doke kungiyar kwallon kafa ta Golden Bullet daci 2 da nema a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a birnin Kano.

Dabo Babes dai rabon dasu lashe wannan gasa tun 1993.

Saidai Dabo Babes kungiyar kwallon kaface mai tarihi inda tsohuwar kungiyar kwallon kafa ce domin kuwa kusan duk sa anninta wato kungiyoyin kwallon kafan da aka kafasu tare duk yanzu babu su.

Wannan wasan karshe ya sami halartar manyan baki daga ciki da wajen jahar nan.

Jaridar Labarai24 ta sami tattaunawa da daya daga cikin masu ruwa da tsaki na wannan kungiya ta Dabo Babes wato Muzammil Dalha Yola “muna godiya ga Allah daya bamu damar lashe wannan gasa ta Premier ta jahar Kano duba da cewa wannan kungiya kusan shekaru 27 basu lashe wannan gasa ba, sannan muna godiya ga sauran masu ruwa da tsaki na wannan kungiya harda ma ‘yan wasa domin duk abubuwan da ake koyamusu na da’a da taka leda yadda ya kamata ya shiga kunnuwansu, haka suma magoya baya muna yabamusu ta yadda ko yaushe suke bibiyar wannan kungiya aduk inda zasuyi wasa da addu’o’i da sukewa wannan kungiya”.

Aynzu dai Dabo Babes sune zakaran wannan gasa ta 2020.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan