Kundin Tarihi: Asalin Yadda Kano Ta Samo Sunanta

  577

  Tarihi ya nuna cewa asalin mutanen da suka fara zama a Kano makera ne da suka taso daga garin Gaya a kokarinsu na neman kasa mai arzikin tama, wacce za su dinga sarrafata su dinga yin karfe da ita.

  Wadannan makera sunyi dace da samun kasa mai wannan arziki, bayan arzikin tama da suka samu, sun kuma samu kasar mai ciki da albarkar noma da ruwa mai yawa ga dazuka da za su iya fita farauta.

  A lokacin wajen ya kasance mai matukar tsaro domin kuwa akwai manyan tsaunika da duwatsu wadanda mutane za su iya hawa su buya idan abokanan gaba sun kawo musu hari.

  Wadannan duwatsu sune irinsu Dutsen Dala, Goron Dutse, Dutsen Fanisau, Jirgirya da kuma Magwan.

  Akwai kuma kogi da ruwa ke wucewa daban-daban da suka zagaye yankin, da suka hada da kogin Jakara da kuma kogin Kano.

  Dalilin wannan arziki na yankin ya sanya mutane suka dinga yin kaura daga garuruwansu suna zuwa wajen domin cigaba da zama.

  Daga cikin mutanen da suka fi shahara a wannan waje akwai wani jarumin mafarauci mai suna Kano, wannan suna na jarumin shine asalin sunan da aka sanyawa garin, tun daga wanan lokacin aka fara kiran wajen da Kano.

  Wani masanin tarihin masarauta dake jami’ar Bayero ta Kano, Dakta Tijjani Muhammad Naniya ya ce har ya zuwa yanzu masana ba su kai ga gano lokacin da mutane suka fara zama a yankin na Kano ba.

  Haka kuma ya ce, masanan basu tantance mutanen wace Gaya ce suka fara zama a wannan waje ba. Ya ce akwai Gaya ta Kano, akwai ta Nijar da kuma ta yankin jihar Sokoto.

  Babu wani cikakken bayani game da lokacin da mutane suka fara zama a yankin Kano, amma dai Dr. Naniya ya ce an taba gano wata makera a kusa da Dutsen Dala da masana suka bayyana cewa ta kai shekara 200 bayan zuwan Annabi Isa.

  Wannan daliline yasa wasu masana ke cewa garin Kano ya samo asali kimanin shekaru 400 kafin zuwan addinin Musulunci. Ma’ana yanzu birnin na Kano ya kai kimanin shekaru kusan 2000 da kafuwa.

  (c) Jaridar Hausa

  Turawa Abokai

  1 Sako

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan