Kwankwaso Ne Ya Murƙushe Kuɗin Ƴan Fansho Naira Biliyan Tara – Shekarau

1585

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya, Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin Hannu Da Yawa da ake gabatarwa a gidan rediyon Najeriya Kaduna.

Sanata Mallam Shekarau ya yi bayani cewa a cikin shekara guda da barinsa kujerar gwamnan Kano, tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya murkushe kudaden da aka tara na ‘yan fansho har naira biliyan tara.

Ko a cikin shekarar 2019 sai da shugaban kungiyar ‘yan fansho reshen jihar Kano Alhaji Salisu Ahmed ya ce fiye da yan fansho dubu uku ke dakon karbar kudaden fanshon su da garatutin su na wadanda suka yi ritaya a shekara ta 2016 zuwa 2018.

A ƙarshe Sanata Shekarau ya ce masu hakki ne ya kamata su binciki inda kayansu yake.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan