An dai haife ta ne a birnin Kano a shekarar 1944, aka yi mata aure tana da shekara 13. Ta rasu tana da shekara 66 a shekarar 2011.
Hajiya Laila Dogonyaro ta shahara wurin fafutukar kare hakkin mata, musamman ganin an ilimantar da su.
Ta shugabanci Majalisar Kasa ta Kungiyoyin Mata a Najeriya, wato National Council of Women’s Societies (NCWS) daga 1993 zuwa 1995.
Kafin haka, tana cikin matan da suka kirkiri Jam’iyyar Matan Arewa da nufin taimaka wa iyalai matalauta a arewacin Najeriya.

Turawa Abokai