Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya ce ba zai miƙa wuya ga matsin lamba ba don sakin Shugaban ‘Yan Shi’a, Ibrahim El-zakzaky.
Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Juma’a da daddare a wata hira ta kai tsaye da jaridar DAILY NIGERIAN ta bibiya a Abuja.
Gwamna El-Rufa’i ya ce gwamnatin jihar Kaduna ta ƙi sassauta wa Shugaban ‘Yan Shi’ar ne saboda al’ummar jihar Kaduna sun sha wahala a hannun Mista El-zakzaky.
“Mun yadda cewa (makomarsa tana hannunmu) amma da gyara. Makomar El-zakzaky ba a hannun gwamnatin jihar Kaduna take ba, tana hannun Babbar Kotun Jihar Kaduna ne. Abinda Gwamnatin Tarayya take nufi a nan shi ne ba ita ta gurfanar da El-zakzaky a kotu ba. Gwamnatin Tarayya ta tsare shi a Abuja bayan rikicin Zariya.
“Yayinda El-zakzaky ke tsare a Abuja, mun zauna mun yi bincike bisa irin karya dokoki, laifuffuka, keta haƙƙi da shi da magoya bayansa suka yi a shekaru 30 da suka wuce a Zariya.
“Bayan kammala bincike, sai muka roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ba mu shi don yi masa shari’a a Kaduna.
“Ba mu ake yi wa kukan mu saki El-zakzaky ba, Gwamnatin Tarayya ake yi wa. Tun lokacin da muka kai shi kotu, ba wanda ya roƙe mu mu sake shi.
“Kuma ba za mu sake shi ba har sai kotu ta wanke shi. Babbar Kotun Jihar Kaduna ce ta bada umarnin a tsare shi a Gidan Yarin Kaduna.
“Shi ne ya buƙaci a kai shi SSS su tsare shi, ba gidan yari ba. Idan mutum yana jiran shar’ia, sau da yawa a gida yari a ke tsare shi. Amma sai ya zaɓi SSS su tsare shi inda ba zai sha wahala ba.
“Tunda SSS suna tsare da shi ba tare da umarnin kotu ba, sai lauyoyinmu suka samo umarni daga kotu da ya ce a mayar da El-zakzaky gidan yari.
“Maganar da muke yi a yanzu, Sheikh El-zakzaky da matarsa suna Gidan Yarin Kaduna, kuma za su ci gaba da zama a can har a kammala sauraron ƙararsu.
“Ba mu san yaushe kotu za ta yanke hukunci ba, amma ba za mu sake shi ba saboda zalunci da shi da mabiyansa suka yi wa al’umma a jihar Kaduna.
“Idan kotu ta wanke shi, ba mu da zaɓi. Amma ba za mu sake shi ba duk kukan da al’umma za su yi, duk zanga-zanga, duk matsin lamba daga ƙasashen ƙetare….suna ɓata lokacinsu ne kawai. Matuƙar ni ne gwamna, ba za a saki El-zakzaky ba har sai an kammala shari’arsa. Amma duk abinda da kotu ta yanke, zan aiwatar da hukuncin”, in ji Gwamna El-Rufa’i.