An Rufe Boda Ne Don A Ceto Tattalin Arziƙin Najeriya -Kwastam

279

Kwanturolan Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa, NCS, Reshen Jihar Kwara, Mohammed Uba Garba ya ce Gwamnatin Tarayya ta rufe bakin iyakokin Najeriya ne don inganta noma a cikin gida, inganta lafiya, tsare bakin iyakokin ƙasar nan, sannan kuma a tilasta ƙasashe maƙobtan Najeriya bin dokokin Hukumar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS.

Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa ta Jihar Kwara, Zakari Chado ya aiko wa Labarai24.

Idan dai ba a manta ba, a cikin makon nan ne Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Onorabul Salihu Yakubu Danladi ya kai ziyara ga Kwanturolan NCS na jihar Kwara, inda ya koka bisa ƙarancin man fetur da garuruwan dake kan iyakan jihar suke fuskanta.

Mista Garba ya kai ziyara garuruwan Alapa, Ilesha-Baruba, Yashkira, Chikanda da Okuta, dukkaninsu a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Baruten ta jihar Kwara.

Mista Garba, wanda ya kuma kai ziyara ga Sarkin Yashkira, ya jaddada irin rawar da sarakunan gargajiya za su iya takawa wajen wayar da kan jama’a, masu ruwa da tsaki da sauran jama’a gaba ɗaya.

“Na kawo ziyara don in sanar da Sarki cewa an turo ni a matsayin Shugaban Rundunar Haɗin Gwiwa ta Bakin Iyakoki, Arewa ta Tsakiya, Shiyya ta Uku, Jihar Kwara, kuma ina so in ƙarfafa kyakkyawar dangantakar da ake da ita tsakanin rundunar, masarauta, masu ruwa da tsaki, mu kuma kira da a samu haɗin kai ta fuskar tattara da musayar bayanai, kuma a cike giɓin sadarwa.

Shugaban ya yi kira da a ruɓanya shirye-shiryen wayar da kai game da yaƙi da shigo da kaya ba bisa ka’ida ba, saboda masu yin hakan ba sa ganin sa a matsayin laifi.

Ya jaddada cewa ba an rufe bakin iyajokin ƙasar nan ba ne don a yi wa halattaccen kasuwanci na ‘yan asalin ƙasar nan bi-ta-da-ƙulli ko a kawo musu tazgaro ba, an yi haka ne don a ƙarfafa gwiwar manoman gida, hana shigo da makamai da albarusai, hana shigo da muggan ƙwayoyi da sauran haramtattun kaya a ciki da wajen ƙasar nan.

Amma ya ce muhimmancin haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro da shugabannin gargajiya ba zai misaltu ba, saboda ba wata hukuma da za ta yi aiki ita kaɗai kuma ta yi nasara ba tare da tallafin ɗayar ba, musamman shugabannin gargajiya.

Da yake mayar da jawabi, Sarkin Yashkira, Umar Sarki Sabikpasi II, ya ce Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa kusan ita ce zuciyar Najeriya idan ana maganar tattara kuɗaɗen shiga, kuma ya nuna goyon bayansa game da rufe bakin iyaka, saboda mafiya yawan masu shigo da kaya ba bisa ka’ida ba a ƙasarsa ba ‘yan Najeriya ba ne.

Ya yi alƙawarin yin duk mai yiwuwa wajen ba Shugaban da tawagarsa goyon baya don su yi nasara ta hanyar samar da bayanai game da aikin da ake kan yi don cimma muradun da aka sa a gaba saboda shigo da kaya ba bisa ka’ida ba abu ba ne mai kyau da za a ƙarfafa.

A ta bakinsa, manufar da ta sa aka rufe bakin iyaka shi ne don tattalin arziƙin Najeriya ya ci gaba.

Ya bada shawarar da a riƙa sa shugabannin gargajiya a cikin al’amura a kodayaushe.

Ya yi kira da a riƙa yin hukunci mai tsanani ga masu yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa, a kuma gano gidajen mai masu lasisi da marasa lasisi, sannan a rufe su.

Mista Garba ya kuma shirya taron ganawa da mutanen gari, inda ya haɗu da matasa, dattawa, ƙaramar hukumar, Ƙungiyar Masu Dakon Man Fetur Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, IPMAN da masu ruwa da tsaki a rufe bakin iyaka na ƙaramar hukumar.

Shugaban ya ɗauki lokaci yana wayar musu da kai bisa alfanu da rashin alfanu na shigo da kaya ba bisa ka’ida ba, da kuma muhimmancin rufe kan iyaka.

“Yawaitar shigowa Najeriya ba bisa ka’ida ba da yawaita laifukan da ake aikatawa tsakanin kan iyaka da kan iyaka kamar shigo da ƙananan makamai, fataucin ɗan Adam, shigo da ƙwaya, ta’addanci da sauransu dole a kawo ƙarshen su ba tare da jinkiri ba, kuma shi ne yasa Gwamnatin Tarayya ta rufe kan iyakokinta”, in ji shi.

Ya nuna cewa zirga-zirga da jarkoki da babu komai a cikin su shi yake haifar da shigo da man fetur ba bisa ka’ida ba, kuma ya zama dole masu wannan ɗabi’a su guje ta.

A ta bakin Mista Garba, dakatar da kai man fetur kilomita 20 kafin garin da yake kan iyaka umarni ne na Shugaban Ƙasar, kuma zai aiwatar da shi.

Ya ƙara da cewa alƙaluman da Hukumar Raya Garuruwan Kan Iyaka ta Ƙasa, BCDA ta fitar sun nuna cewa Najeriya ta yi iyaka da ƙasashe huɗu a jihohi jihohi 21 daga cikin 36.

Haka kuma, akwai iyakokin ƙasashen waje a garuruwa 300, ƙananan hukumomi 105, waɗanda Baruten ɗaya ce kawai daga cikin waɗanda suke da boda ta ƙasar waje.

Ya ƙara da cewa yawan aikata laifuka ya ragu sosai tunda aka fara rufe kan iyakoki.

A lokacin ganawar da al’ummar gari, an bayyana cewa ƙaramar hukumar Baruten ta jihar Kwara tana da yawan al’umma da ya kai 125,000, da gidajen mai fiye da 200.

Wakilin shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Tamba Ahmed da Shugaban IPMAN, Reshen Jihar Kwara, Alhaji Okonlawon Olarewaju ya yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa ɗaukar wannan mataki na gyara kuskuren da gwamnatocin baya suka yi, ba kamar manufofin baya ba da ba a aiwatar da su.

Duka su biyun sun yi kira ga NCS da ta ƙara duba hana kai man fetur kilomita 20 kafin garin da yake kan iyaka.

Da yake bayani game da yawan gidajen mai dake ƙaramar hukumar, Shugaban na IPMAN ya ce kamfanoni 65 ne kaɗai suka yi rijista da ƙungiyar, kuma wasu kamfanonin suna da gidajen mai fiye da biyar.

Mista Garba ya faɗa wa taron cewa NCS mai aiwatar da manufofin Gwamnatin Tarayya ce kawai.

Ya shawarci ƙaramar hukumar da ta yi aiki da Kakakin Majalisar wanda shi ma ɗan asalin karamar hukumar ne da sauran ƙusoshin gwamnati don shigar da ƙorafe-ƙorafensu inda ya dace.

Ya tabbatar da cewa zai gabatar da rahotonsa ne “kan abinda ya gani”.

A ta bakinsa, ya yi imanin cewa tabbas gwamnati za ta kawo manufar da za ta amfani kowa.

Mista Garba ya kuma haɗu da hukumomin tsaro masu lura da kan iyaka na yankin da kuma jami’an ‘Joint Border Operation Drill’ da suka a kan iyakar.

Ya karanta musu dokar da ta hana bijirewa, yana mai neman samun haɗin kai ta hanyar musayar bayanai don cimma manufar Gwamnatin Tarayya na rufe kan iyakar.

Ya yi gargaɗin cewa duk jami’in da aka samu yana ɗungushe ko wasa da aiki zai fuskanci fushin doka.

Shugaban na NCS ya bayyana cewa dukkan jami’an tsaro da suke aiki don tabbatar da aiki da rufe kan iyakar suna da goyon bayan Dokar Gudanar Da Aikin Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa, CEMA, Sashi na 158, 147 da 167 wanda ya ce Sashi na 158 ya bada iko a yi sintiri ba tare da ƙa’ida ba, amma ya hana mutum ɗaya ya yi sintiri.

Sashi na 147 ya bada iko da a yi bincike a kuma yi dirar mikiya a duk wata haraba da ake zargin akwai kayan da aka shigo da su ba bisa ka’ida ba, kuma Shugaban zai bada izini a je a binciki irin waɗannan wurare.

Sashi na 167 ya bada iko a tsare a kuma ƙwace kayyaki.

Mista Garba ya bada umarnin a bada rahoton duk wani abu cikin gaggawa don ɗaukar mataki.

Ya yi kira gare su da su yi aiki da al’umomin da suka karɓe su, su girmama al’adunsu don kawar da shigo da kaya ba bisa ka’ida ba a ƙasar nan, saboda hakan zai bunƙasa samar da kayan gida, ya kuma samar wa da gwamnati ƙarin kuɗin shiga ya kuma samar wa da ɗimbin matasa aikin yi.

Mista Garba ya yi kira ga hukumomin tsaro da su yi aiki tare don cimma wannan manufa, yana mai tunatar da su tanade-tanaden Sashi na 177 na CEMA, wanda ya tanadi horon zaman gidan yari na shekara biyu ga duk wanda ya taimaka aka shigo da kaya ba bisa ka’ida ba.

Kwanturolan ya kuma duba kayayyaki masu tarin yawa da aka ƙwace a Okuta, Ilesha-Baruba da Chikanda.

Ana sa ran za a Kwanturolan zai ci gaba da ran gadi da shirin wayar da kai a garuruwan Kiama a jihar Kwara; Wawa/ Babanna a jihar Naija da Ogoja/Adipo a jihar Benue.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan