An Kwantar Da Gwamnan Bauchi A Asibitin Birnin Landan

194

Yanzu muke samun rahoton cewa an kwantar da Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed Kaura a wani asibiti dake birnin Landan sanadiyyar rashin lafiya da har yanzu ba a bayyana kowacce iri bace.

A wata sanarwa da mataimakin gwamnan na musamman a fannin yada labarai, Mukhtar Gidado ya fitar ga manema labarai jiya a Bauchi, ya bayyana wani sako da gwamnan ya aikowa da al’ummar jihar a kan zaman da kotu za tayi game da kalubalantar kujerarsa, gwamnan ya aiko da sakon ne a lokacin da yake kwance a gadon asibiti a birnin na Landan.

Sanarwa ta ce: “Ina asibiti, amma na tabbata Allah zai bamu nasara a kotu, nasara ta mu ce Insha Allah.”

Sanarwar ta sake tabbatar da kudurin gwamnatin jihar na kyawawan manufofinta akan al’ummar jihar, inda suka yi alkawarin yin adalci.

Bayan haka gwamnan yayi alkawarin sakawa mutanen da suka tsaya sau da kafa wajen ganin ya isa wannan matsayi da yake kai a yanzu.

A cewar shi, jinkirin da kotun koli tayi wajen yanke hukunci akan shari’arsu, lokaci ne da Allah ya nuna masa ainahin mutanen dake kaunarsa da kuma wadanda ke munafurtarsa.

Gwamnan ya mika godiyarsa ga mutanen da ya kira da masu goyon bayansa da kuma kishin jihar da ma kasa baki daya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan