Rashin Takardun Gwajin Jini Ya Hana Ɗaurin Aure A Kano

595

Al’amarin dai ya faru ne a kauyen Bundum mazabar wangara dake karamar hukumar Tofa a jihar Kano, bayan an gabatar da takardar gwajin jinin Amarya wadda ta tabbatar da lafiyar ta, sai limamin daurin auren, Muhammad Lawan ya tambayi cikakkun takardun shedar gwajin jinin Ango waliyan sa suka ce babu, shi kuma limamin, ya ce ba zai daura auren ba har sai inda takardun.


Jin wannan batun ne shima waliyin Amarya mai suna Sani Inuwa da sauran madaura auren suka goyi bayan lallai sai an kawo takardun gwajin jinni na Angon sannan za a daura auren.


Wannan al’amarin dai ya matukar tada hankalin waliyan Ango Kabiru Ibrahim, nan take ya tuntubi Angon Abdurrashid Shehu, nan take ya ce” Ya yi gwajin jinin amma takardar sakamakon ne aka manta ba’a tafi da ita ba wurin daurin auren”.

Wannan ya sanya ba a daura auren ba a lokacin har sai da aka jira a akaje aka dauko takardun, aka kuma tabbatar ta lafiyar Angon ce sannan aka daura auren.


Wasu rahotanni sun rawaito cewa cikin ‘yan kwanakin nan a yankin na Tofa, sau biyu aka fasa daurin aure kwata-kwata, bayan an riga an taru, na farko sabida takardar gwajin jini ta nuna cewar Amaryar na dauke da juna biyu, karo na biyun kuma takardar gwajin jinin ta nuna cewar Angon na dauke da cuta me karya garkuwar jiki wato (HIV).

Rahoton Dala FM Kano

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan