Jami’an hukumar da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa a jihar Kano wato KAROTA sun yi nasarar cafke wani Ɗan KAROTA na bogi wanda yake gudanar da harkokinsa a kasuwar Kantin Kwari a Kano
Wannan dan karotar Bogi mai Suna Sulaiman Haladu an kama shi ne a kasuwar kantin kwari lokacin da yake gudanar da dabi’arsa ta karbar kudi a hannun direbobin motar da suke kokarin fita daga kasuwar Kwari
Bincike ya nuna cewa shi dan karotar bogin dan asalin jihar Katsina ne a inda yake kwana a cikin kasuwar Kantin kwari
Dan karotar bogin yace sun jima suna gudanar da wannan al’adar sai yanzu dubunsa ta cika.
Tun farko dai Hukumar ta KAROTA ta karbi ƙorafe-ƙorafe ne daga wasu daga cikin yan kasuwar ta kwari,
Inda Hukumar ta tura jami’anta na sirri dan gano da kuma bankaɗo masu aiwatar da wannan dabi’a
Hukumar ta KAROTA ta mika shi hannun jami’an ‘Yansanda domin a ƙara faɗaɗa bincike.
