Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Ya Tsallake Rijiya Da Baya

174

Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, ya gamu da fushin wasu matasan da suka halarci zaman kotun kolin Najeriya a Litinin.

Bayan zaman da kotu tayi, tsohon gwamnan ya fito daga cikin kotu yana ɗaga hannunsu na gaisuwa ga mabiyansa kawai sai wasu suka fara jifansa da duwatsu da gorunan ruwa.

Daily Trust ta ruwaito. Yayin da jami’an tsaro suka yi awon gaba da shi gudun kada ji masa rauni, sai matasan suka bi shi suna masa ihu “Karya ne” “Barawo”

Ana kyautata zaton mabiya abokin hamayyarsa, Gwamna Bala Mohammed, suka aikata wannan aika-aikan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan