Ajiya Litinin ne wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace Alhaji Adam Muhammad Sarkin Yamma, dagacin Karshi dake cikin karamar hukumar Rogo ta jihar Kano.
An ruwaito cewa ‘yan bindigar sun shiga a cikin dakin mai garin da misalin karfe 3 na dare suka yi awon gaba dashi.
A cewar wani abokinshi mai suna Auwal Mustapha Iman, har ya zuwa yanzu barayin basu kira iyalin mai garin ba a waya.
“An sace abokina Adam Muhammad Sarkin Yamma jiya da daddare. Barayin sun shiga har cikin uwar daka da karfe 3 na dare suka sace shi, sun sace shi a kauyen Karshi dake cikin karamar hukumar Rogo, kuma shine mai garin na Karshi dake cikin jihar Kano. Har yanzu basu kira ba game da kudin fansa, kuma duka layikan wayarshi a kashe suke.
“Dan Allah ku sanya shi a addu’a, kuma ku kai rahoto idan an ga wani abu da ba’a gane ba dangane dashi. Allah ya fito mana dashi, ya kuma tona asirinsu. Amin
Kawo haɗa wannan rahoton mun yi ƙoƙaein tuntuɓar kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, akan faruwar lamarin. Sai dai hakan ya ci tura sakamakon tangarɗar na’ura.
